”Yan sanda a Zariya sun yi nasarar kama dan fashi da kayan soja

A safiyar Lahadin da ta gabata, ofishin ’yan sanda da ke danmagaji suka kama dan fashi cikin kayan soja da kuma bindiga kirar AK47. Wani jami’in tsaro da bai so a ambaci sunansa ba, ya yi wa Aminiya bayanin cewa: “Misalin karfe uku na dare muka sami labarin cewa wasu gungun ’yan fashi sun tare […]

”Yan sanda a Zariya sun yi nasarar kama dan fashi da kayan soja

A safiyar Lahadin da ta gabata, ofishin ’yan sanda da ke danmagaji suka kama dan fashi cikin kayan soja da kuma bindiga kirar AK47.

Wani jami’in tsaro da bai so a ambaci sunansa ba, ya yi wa Aminiya bayanin cewa: “Misalin karfe uku na dare muka sami labarin cewa wasu gungun ’yan fashi sun tare hanyar Kaduna zuwa Zariya, a yankin Dumbi da ke karamar Hukumar; Zariya sai muka dauki damara tare da ’yan sanda na musamman da muka tanada domin yaki da masu manyan laifuka, muka tunkare su.”

Majiyar ta kara bayyana cewa sun dauki lokaci suna musayar wuta da su, kafin Allah Ya ba su sa’a. “Bayan lokaci muna artabu da su sai can muka ji daga bangaran ’yan fashin sun dauke wuta, sai kuma muka ji ihu ana cewa Abdullahi ka taimake ni. To, ashe daya ne daga cikinsu da muka harba, su kuma sauran sun gudu.

“Bayan lokaci sai muka isa wurin da muke jin ihu sai muka kama daya daga cikinsu mai suna Umar Sani sanye da cikakken kayan sojan Najeriya da kuma wata babbar bindiga samfurin AK47, kuma ciki da harsashi a cikinta.”

Majiyar ta kara da cewa wanda aka kama mai suna Umar Sani ya yi bayanin cewa wani ne mai suna Abubakar ya gayyato shi daga Jihar Taraba domin su zo su rika yin fashi kuma kafin su zo inda za su taru, sun zauna a Marabar Jos. Ya ce su takwas ne suka zo kuma dukkansu suna da kayan sojoji da bindigogi kirar AK47 guda hudu, wadanda suka zo da su wurin yin fashin. Ya shaida cewa kusan duk an sami wasu daga cikinsu da harbi sai dai ’yan uwansa sun kwashe su sun tafi da su.

Mataimakin kwamishinan ’yan sanda mai kula da shiyya ta daya, Abdullahi Ibrahim, wanda shi ne ya jagoranci rundunar, ya ce sun kai wanda aka harba asibiti an samar masa magani kuma ya yi kira ga cibiyoyin kula da lafiya a ko’ina cewa, idan sun ga wani da raunin bindiga to a sanar da su, domin suna zaton wasu daga cikin ’yan fashin sun tafi da raunin harbi a jikinsu.