’Yan sanda na bincike kan salwantar kudin maniyyata a Neja

Sashin Binciken Manyan Laifuffuka na Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja ya fara bincike kan salwantar kudin maniyyatan aikin Hajjin bara na karamar Hukumar Bosso ta hannun Jami’in Kula da Maniyyatan yankin, Ahmad Bawa Barkuta.’Yan sandan sun gayyaci tsohuwar Shugabar karamar Hukumar Hajiya Ladidi Bawa Bosso zuwa ofishinsu domin bayar da bayanan da za su taimaka […]

’Yan sanda na bincike kan salwantar kudin maniyyata a Neja
’Yan sanda na bincike kan salwantar kudin maniyyata a Neja

Sashin Binciken Manyan Laifuffuka na Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja ya fara bincike kan salwantar kudin maniyyatan aikin Hajjin bara na karamar Hukumar Bosso ta hannun Jami’in Kula da Maniyyatan yankin, Ahmad Bawa Barkuta.
’Yan sandan sun gayyaci tsohuwar Shugabar karamar Hukumar Hajiya Ladidi Bawa Bosso zuwa ofishinsu domin bayar da bayanan da za su taimaka musu wurin gano dalilai da hanyoyin da aka bi fiye da Naira miliyan 37 suka yi layar zana bayan da maniyyatan suka biya kudin amma hakan ya sa suka rasa zuwa aikin Hajjin bara.
’Yan sandan sun bayar da belin tsohuwar shugabar a karshen mako bayan da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP, Tanko Beji ya tsaya mata tare da alkawarin kawo musu ita a duk lokacin da suka bukata.
Shi kuwa Alhaji Ahmad Bawa Barkuta ya ci gaba da gudun hijira, inda bayanai suka nuna cewa ba a san inda yake ba, balle a kama shi.
Alhaji Ahmad Bawa Barkuta wanda a yayin da lamarin ya auku ya ce wasu mutane ne suka yi masa barazanar kisa muddin bai ba su kudin maniyyatan da ke hannunsa ba. Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jihar Neja ta yi ta daukar matakan ganin an kawo karshen wannan lamari.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja DSP Bala Elkana ya ce, jami’ansu ba za su yi kasa a kwiwa ba sai sun gudanar da cikakken bincke kan lamarin, inda ya ce sun lashi takobin daukar duk matakan da suka kamata domin kwato wa jama’ar da aka zalunta hakkinsu.