’Yan sanda na binciken jami’anta 3 kan zargin fashi a Abuja
Rundunar ’Yan sandan Abuja tana gudanar da bincike a kan jami’anta uku kan zargin hannunsu a fashi da kwace motoci a yanikn Birnin Tarayya, Abuja. Aminiya ta samu labarin cewa wadanda ake zargin biyu daga cikinsu masu kananan mukamai ne da ke aiki a bangaren ’yan sandan kwantar da tarzoma na 50, sai kuma na […]
Xaliban da suka yi sauka
Rundunar ’Yan sandan Abuja tana gudanar da bincike a kan jami’anta uku kan zargin hannunsu a fashi da kwace motoci a yanikn Birnin Tarayya, Abuja. Aminiya ta samu labarin cewa wadanda ake zargin biyu daga cikinsu masu kananan mukamai ne da ke aiki a bangaren ’yan sandan kwantar da tarzoma na 50, sai kuma na ukun mai babban mukami da ke aiki a daya daga cikin manyan ofisoshin ’yan sanda, duk a garin Kubwa.
Babban Kakakin Rundunar, ACP Anjuguri Manza wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an mika lamarin ga sashin binciken manyan laifuffuka (CID).
Tun farko majiyar Aminiya ta ce, daya daga cikin ’yan sandan ya kwace wata mota ce tare da wasu abokan huldarsa farar hula da dare a garin Kubwa, bayan nan sai ya je wani masaukin baki a garin, ya kama daki.
Majiyar ’yan sandan ta ce, sai aka samu akasi wanda ya kwace wa motar shi ma ya je gidan kuma lokacin da ya shigo bayan ya kama dakin sai ya sanar da daya wani babban ofishin ’yan sanda na garin inda jami’ansu suka kutsa gidan suka kama shi.
Bayanai sun ce an gano bindiga kirar AK 47 a cikin motar da ya shigo da ita, wadda aka ce ta babban dan sandan da suke hulda tare ne.
Wanda ake zargi na uku, bayanai sun ce babban wanda ake zargi ne da bayar da aron bindgarsa lokacin da ba ya aiki kuma ya mayar da bindigar ofishinsu. Tuni aka gano motoci shida daga hannun wadanda ake zargin baya ga sauran abubuwa, kamar yadda majiyar ta bayyana.