’Yan sanda na binciken mawaki Davido kan mutuwar abokinsa

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta gayyaci fitaccen mawakin nan mai suna Davido Adekeke wanda ake yi wa lakabi da Davido kan domin ya amsa wasu tambayoyi a kan mutuwar abokinsa mai suna Tagbo. Wasu da ba a gano ko su waye ba sun ajiye gawar Tagbo a cikin mota kirar kamfanin Toyota a bakin […]

’Yan sanda na binciken mawaki Davido kan mutuwar abokinsa

Rundunar ’yan sandan Jihar Legas ta gayyaci fitaccen mawakin nan mai suna Davido Adekeke wanda ake yi wa lakabi da Davido kan domin ya amsa wasu tambayoyi a kan mutuwar abokinsa mai suna Tagbo.
Wasu da ba a gano ko su waye ba sun ajiye gawar Tagbo a cikin mota kirar kamfanin Toyota a bakin kofar babban asibitin jihar.
Lamarin ya mamaye kafar sadarwa ta sa da zumunta mako biyu da suka gabata yayin da budurwar marigayin mai suna Caroline ta watsa a shafin Instigram dinta tana zargin Davido da kashe saurayinta nata.