’Yan sanda na binciken yadda dalibin jami’a ya rataye kansa a Bauchi

dalibai da malaman Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi sun samu kansu cikin firgici, lokacin da suka wayi gari suka sami gawar dalibin jami’ar mai Suna dahiru Adamu rataye a jikin bishiya kuma ga takardun karatunsa a gefe a harabar jami’ar da ke Gubi, kan hanyar zuwa Kano.  Al’amarin, wanda a yanzu haka ’yan […]

’Yan sanda na binciken yadda dalibin jami’a ya rataye kansa a Bauchi

dalibai da malaman Jami’ar Abubakar Tafawa balewa da ke Bauchi sun samu kansu cikin firgici, lokacin da suka wayi gari suka sami gawar dalibin jami’ar mai Suna dahiru Adamu rataye a jikin bishiya kuma ga takardun karatunsa a gefe a harabar jami’ar da ke Gubi, kan hanyar zuwa Kano.  Al’amarin, wanda a yanzu haka ’yan sanda ke kan binciken musabbabinsa, ya sanya hukumomin jami’ar da al’umma cikin jimami da firgici.

A zantawarsu da manema labarai, malamai da daliban jami’ar sun ce marigayi dahiru Adamu dalibi ne da ke karatun sana’ar hannu na kere-kere da kafintanci kuma yana aji uku ne a Tsangayar Koyon Ilimin Fasaha da ke jami’ar. Sun bayyana cewa ana zargin mamacin ya rataye kansa da kansa ne, domin an wayi gari da ganin gawarsa a rataye ba tare da sanin hakikanin abin da ya haddasa shi daukar wannan mataki ba.

Binciken Aminiya ya kalato cewa, lokacin da malamai da daliban suka shiga makarantar ne da safe sai suka ga gawar mamacin tana lilo a rataye a jikin bishiya, wanda hakan ya nuna cewa ya dade da mutuwa. “Muna tunanin a cikin dare ne ya rataye kansa,” inji su.

An same shi ne yana sanye da riga jamfa, kansa rataye da igiyar tsumma mai karfi a kusa da Tsangayar Nazarin Al’amuran Gudanarwa ta Jami’ar. daliban suka ce daga bisani aka sanar da hukumar jami’ar, inda jama’a suka taru suna kallon gawar har da manya da kananan jami’ai na makarantar. Daga bisani aka zo da motar daukar asibiti, kafin daga bisani aka kai rahoto ga ’yan sanda, suka zo suka kwnce shi, suka dauki gawar zuwa asibiti.

A kusa da inda ya rataye kansa, wadanda suka shaida gawar tasa sun ga takalmansa da kuma littafai da alkalamin rubutunsa a jikin bishiyar da yake rataye, kodayake bai rubuta wani dalili da ya sa ya kashe kansa ba.

Kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Bauchi, DSP Kamal Datti Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya kuma shaida cewar yanzu haka suna nan suna ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, domin gano musabbabin mutuwarsa.

Ya ce abin da ya tabbata dai shi ne: “An sami gawarsa a rataye amma bincikenmu na ci gaba da gudana. Yanzu haka ba zan iya tabatar maka cewar kashe kansa ya yi ko kuma kashe shi aka yi ba amma binciken likitoci da kuma namu na ’yan sanda shi ne zai tabbatar mana da mene ne musabbabin mutuwar tasa.”

Ya ce mamacin zai kai shekara talatin 30 da haihuwa kuma dan jihar Bauchi ne da ke da zama a Unguwar kofar dumi da ke cikin garin Bauchi.”

Kodayake wadansu daga cikin abokan karatunsa na hasashen cewa marigayin bai samu halartar horon sanin makamar aiki da dalibai ke zuwa ba na shekara guda ba kuma zai gyara wasu daga cikin darussan da bai ci sosai ba a makarantar,  kodayake binciken da hukumomi ke yi ne kawai zai tabbatar da gaskiyar yadda abin da ya auku.