‘Yan sanda na farautar sanatoci a Amurka
Takaddama ta kaure a zauren Majalisar Jihar Oregun ta kasar Amurka bayan da wadansu sanatoci ’ya’yan Jam’iyyar Republican suka shiga wasan buya da ’yan sanda. ’Yan majalisar da suka fice daga zauran Majalisar Dokoki a Salem babban birnin jihar a ranar Alhamis din makon jiya, an ba ’yan sanda umarnin su kamo su. Wannan al’amari […]
Takaddama ta kaure a zauren Majalisar Jihar Oregun ta kasar Amurka bayan da wadansu sanatoci ’ya’yan Jam’iyyar Republican suka shiga wasan buya da ’yan sanda.
’Yan majalisar da suka fice daga zauran Majalisar Dokoki a Salem babban birnin jihar a ranar Alhamis din makon jiya, an ba ’yan sanda umarnin su kamo su.
Wannan al’amari ya faru ne bayan sabani a tsakanin bangarorin jam’iyyun siyasar da ke hamayya a jihar.
’Ya’yan Jam’iyyar Democrat da ke da rinjaye a majalisar, suna son amince da dokar sauyin yanayi, amma ’ya’yan Jam’iyyar Republican suka fice don haramta aukuwar haka.
’Yan Democrat a Oregun na son jihar ta zama ta biyu da ta amince da dokar sauyin yanayi a kasar Amurka.
Dokar ta shekarar 2020 na son rage yawan gurbatacciyar iskar da masana’atun jihar ke fitarwa zuwa kashi 80 a shekara ta 2050, kasa da matakin shekarar 1990.
A karkashin dokar, ana sa ran farashin man fetur da gas zai karu. Sai dai ’yan Republican na ganin wannan sauyin yanayi zai fi shafar mutanen karkara ne musamman manoma.
’Yan adawar sun nemi a yi zaben raba-gardama, domin ba wa dukkan mutanen jihar damar bayyana ra’ayinsu game da matakin.
Jam’iyyar Democrats dai tana da yawan kujerun sanatoci 18 cikin 30 a jihar, amma dole sai sanatoci 20 na zauren majalisar sun hallara kafin a iya jefa kuri’a. Su dai sanatocin Jam’iyyar Republican 11 sun kaurace wa zaman majalisar ce don hana aiwatar da kudirin dokar.
Gwamnan Jihar Oregun wadda ’yar Jam’iyyar Democrat ce, Kate Brown, ta ba ’yan sanda umarnin su gano inda sanatocin suka buya, domin su dawo su yi aikin da aka zabe su dominsa.
’Yan Republican sun fitar da wata sanarwa inda suka bayyana dalilin kaurace wa zauren majalisar. Sun ce “Al’ummar Oregon sun cancanci tsari mafi kyau, lokaci ya yi da jam’iyyar da ke da rinjaye za ta yi la’akari da dukkan mutanen Oregon”- ba kawai wadanda ke Portland ba, inji Shugaban sanatocin Republican Herman Baerschiger Jr.