’Yan sanda na farautar ’yan Shi’a kan Kisan ’yan sanda a Abuja

’Yan sanda biyu wani ɗan kasuwa aka kashe a rikicin da ya ɓarke a Kasuwar Wuse da ke birnin Abuja

’Yan sanda na farautar ’yan Shi’a kan Kisan ’yan sanda a Abuja

Shugaban ‘yan sandan Najeriya

Shugaban ’Yan Sanda Najeriya, Kayode Egbetekun, ya umarci rundunar ta farauto mabiya aƙidar Shi’a ’yan ƙungiyar IMN da suka hallaka ’yan sanda a Abuja.

A ranar Lahadi ne dai ’yan sanda biyu suka kwanta dama a Abuja, a yayin arangama da ’yan ƙungiyar ta IMN a Kasuwar Wuse da ke birnin Abuja.

An kuma kashe wani dan kasuwa tare da koma motocin ’yan sanda akalla guda uku a yayin rikicin kasuwar.

Ƙungiyar IMN ta bayyana cewa ita ma ta rasa mambobinta da dama da ba a tantance adadinsu ba, a yayin ɗauki-ba-daɗin.

Da yake sanar da umarnin shugaban ’yan sandan, Kakakin ’yan sandan Najeriya, Muyiwa Adejobi ya bayyana cewa zuwa yanzu mutum 97 na hannun rundunar kan zargin hannunsu a kisan ’yan sandan.

Ya kara da cewa rundunar za ta ci gaba da bincike domin gano ainihin abin da ya faru da kuma  tabbatar da adalci ga jami’an da aka kashe.

Tuni kwamishinan ’yan sanda na yankin Babban Birnin Tarayya, Kenneth Igwe, ya bayyana takaicinsa kan kisan jami’an rundunarsa da ka a yi a rikincin.

Ya kara da cewa ba zi yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an kamo tare da hukunta duk masu hannu a ciki.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja