‘Yan sanda na neman direban da ya kashe dan sanda

Direba ya kade dan sanda da mota a Jihar Ekiti a lokacin da jami’in ke hanyarsa ta zuwa aiki

‘Yan sanda na neman direban da ya kashe dan sanda

Jami’an ‘Yan sanda

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ekiti na neman wani direba da ake zargi da buge wani dan sanda da mota lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Dan sandan  wanda ke aiki a caji ofis in yankin Aramako ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa aiki a ranar Asabar 3 ga watan Oktoba.

Mai Magana da Yawun Rundunar  ’Yan Sandan Jihar Ekiti, Sunday Abutu ya shaida wa manema labarai cewa rundunar ta kaddamar da bincike, tana kuma aikin neman direban da ake zargi da buge jami ’in nata.

Abutu ya ce dan sandan baya rike da makami a lokacin da direban ya kade shi a kan hanyar Ifon daga Aramako, ya kuma mutu ne sakamakon raunin da ya samu daga kade shi da motar ta yi.