’Yan sanda na neman masu tunzura Ale Rufai Mai Gangaliyon

Kwamishian ’yan sandan Kano ya bayar da umanin ne bayan lauyoyi sun kai wa rundunar korafi

’Yan sanda na neman masu tunzura Ale Rufai Mai Gangaliyon

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta umarci jami’anta su kamo masu yada bidiyon matashin nan, Alhaji A.A. Rufai, wanda aka fi sani da Ale Rufai Mai Gangaliyon a Soshiyal Midiya.

Kwamishian ’yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel ya bayar da umanin ne bayan lauyoyi sun kai wa rundunarsa korafi kan masu yada bidiyon Ale Rufai, bayan ’yan uwansa sun tabbatar cewa yana da larura kwakwalwa.

Kakakin Rundunar SP Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

Wane ne Ale Rufai?

Bidiyon Ale Rufai sun karaɗe soshiyal midiya a baya-bayann an inda yake ambaton adadin kuɗi da suka zarta hankali irinsu Gangaliyon da Auwaliyon.

Matashin wanda yake ciniki a Kasuwar Kurmi da ke birnin Kano ya samu lalurar ƙwaƙwalwa ne tun yana makarantar sakandare.

Duk da cewa halin da Ale Rufai ke ciki akwai alamun matsin rayuwa, yana riya cewa babu wani mai kuɗi da ya kai shi  a duk duniya.

Wannan ya sa ƴan soshiyal midiya suke ta yi masa bidiyo yana sayen manyan kamfanoni da muhimman wurare, inda

Kawo yanzu dai idan aka daka ta waɗanann bidiyoyin, Ale Rufai ya saye jihohin Kano, Kaduna da Jigawa, gami da kamfanonin Ɗangote da BUA.

Neman Magani

Bayan da bidiyoyin suka yaɗu sai kuma wasu masu jin ƙai suka fara neman haɗa gidauniya domin tallafawa a nema masa magani.

A nan ne ƴan uwansa suka magantu a shafukan Facebook da ma gidajen rediyo a Kano, inda suka ce suna yin iya bakin ƙoƙarinsu na kula da shi.

Shirin zuwa kotu

Da safiyar Litinin ne kuma, Barista Abba Hikima ya gargaɗi masu tunzara shi cewa zai gurfanar da su gaban shari’a idan ba su daina ba.

A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Abba Hikimi ya ce likitoci sun tabbatar cewa tsokanar da ake masa na ƙara masa rashin lafiyar dake damunsa.

Ya ce “Wannan rashin tsari ne da sanin ya kamata. Inda ɗan uwan masu yin hakan ne babu wanda zai bari a dinga wulaƙanta shi haka.