’Yan sanda na neman mukarrabin Shekarau kan laifin zabe

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta ce tana neman wani tsohon kwamishina a lokacin mulkin tsohon Gwamnan Kano kuma Ministan Ilimi Malam Ibrahim Shekarau saboda zarginsa da ikaata laifin da suka shafi zabe. Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Ibrahim K. Idris ya bayyana wa manema labarai cewa tsohon Kwamishinan shi ne Musa Iliyasu Kwankwaso.Kwamishinan ya ce […]

’Yan sanda na neman mukarrabin Shekarau kan laifin zabe
’Yan sanda na neman mukarrabin Shekarau kan laifin zabe

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta ce tana neman wani tsohon kwamishina a lokacin mulkin tsohon Gwamnan Kano kuma Ministan Ilimi Malam Ibrahim Shekarau saboda zarginsa da ikaata laifin da suka shafi zabe.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Ibrahim K. Idris ya bayyana wa manema labarai cewa tsohon Kwamishinan shi ne Musa Iliyasu Kwankwaso.
Kwamishinan ya ce wani Hussaini Adamu, mazunin garin kauran Mata a yankin karamar Hukumar Madobi ne ya jagoranci wasu matasa18 dauke da makamai inda suka kwace takardun zabe tare da yayyaga su. Haka kuma matasan sun kone wasu takardun da aka tanada don yin zaben gwamnoni da ’yan majalisar jiha.
Kwamishinan ya ce wadanda aka kama din ne suka bayyana sunan tsohon Kwamishina Musa Iliyasu Kwankwaso a matsayin wanda ya dauki nauyinsu don su gudanar da wannan aika-aika.
A cewar Kwamishinan ’Yan sandan, “Wanda ake zargi da daukar nauyin masu ta’addancin ya cika wa wandonsa iska a lokacin da jami’anmu suka je gidansa don kama shi, inda ya tsallake katanga ya bar babbar rigarsa. Har yanzu muna nemansa da sauran wadansu mutum hudu da har yanzu ba a gan su ba.”
Rundunar ’Yan sandan ta ce ta kame wasu ma’aikatan wucin-gadi na Hukumar Zabe saboda samunsu da laifuffuka daban-daban a kokarinsu na karkatar da kayyayakin zabe.
A cewar Kwaminshinan “Wadanda aka kama sun hada da A’isha Zubairu a karamar Hukumar Takai inda ake zarginta da hadin baki wajen karkatar da kayayyakin zabe zuwa
gidanta. Haka akwai batun wadanda aka kama da laifin tayar da tarzoma a wajen kada kuri’a inda suka sace kayyakakin zabe a kananan hukumomin Shanono da Rano da Tofa da Gabasawa da garin Kwanar dangora.”
Rundunar ta ce za ta hada kai da Hukumar Zabe ta kasa wajen gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu kamar yadda yake kunshe a cikin kundin dokar zabe ta kasa.