’Yan sanda na neman wanda ya sari wuyan abokinsa a Benin
‘Yan sandan shiyyar Eyaen suna neman wani matashi mai suna Hasan Taraba mai shekara 25, dan asalin Jihar Taraba, wanda ake zargin ya sare wa abokin aikinsa na kura- kura wuya da adda, mai suna AbdulAziz Musa, mai shekara 18, kuma dan asalin yankin Zariya ta Jhar Kaduna ne.Lamarin ya faru ne a tsakanin wadannan […]
‘Yan sandan shiyyar Eyaen suna neman wani matashi mai suna Hasan Taraba mai shekara 25, dan asalin Jihar Taraba, wanda ake zargin ya sare wa abokin aikinsa na kura- kura wuya da adda, mai suna AbdulAziz Musa, mai shekara 18, kuma dan asalin yankin Zariya ta Jhar Kaduna ne.
Lamarin ya faru ne a tsakanin wadannan matasan biyu, a yayin da suka kaure da hatsaniya a wani gidan Barasa daura da babban titin garin Benin zuwa Auchi, a wani layi da ake kira 2+2, a Unguwar Eyaen da ke kan iyaka tsakanin karamar Hukumar Uhonmwode da Ikpoba Okha jihar Edo.
Ance a lokacin, shi Hasan Taraba da wannan abokin nasa Abdul-aziz Musa suka yi wa wani gidan giya sammako kafin su tafi aikin kura-kura, kamar yadda suka saba, sai suka je suka dirki barasa, har sai da ta kai musu iyaka suka bugu tatil.
A cewar abokin aikinsu na leburanci Dauda danbaba ya yi karin bayani ya ce ‘’Muna nan da sanyin Safiya sai Hasan da shi Abdulaziz suka shiga gidan barasan suka jima, suka fito, sai na ga suna nuna wa juna yatsa, tare da zagin juna sai na rugo na zan raba su, amma sai suka ki saurarena, inda shi Hasan ya zabura da adda da ke kafadarsa sai ya nufi AbdulAziz, ya kai masa sara a wuyansa, da ya ga ya zubar da shi sai kawai ya ranta ana kare ’’.
’Ban san Hasan ya kulla a zuciyarsa zai kashe ni ba a zaman da muke tare da shi, na dauke shi a matsayin aminina; wani abu bai taba ya hada ni da shi ba, ko ya shiga tsakanimu ba. Muna tafiya aikin leburanci tare kawai, yau ga shi kun gani abin da Hasan ya yi mini yana son zai kashe ni, amma Allah ya isa na bar shi da Allah,” inji shi.
A yanzu haka shi Abdulaziz an dauke shi zuwa aka kai shi wani asibiti mai zaman kansa a Benin kuma Babban likita na wannan asibitin ya ce ‘’AbdulAziz ya fara samun sauki duk da cewa dinkin wuyar ya ba mu wahala, amma mun yi irin hikimarmu na likitoci muka dinke masa,” inji Dokta Douke.
Mista Jemis jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda shiyyar, Eyaen ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda ya ce akwai wasu samari biyu dayan mai suna Hasan Taraba, wanda ya gudu muna nemansa, saboda ya yi amfani da makami na gargajiya (adda) ya sari wa abokin aikinsa mai suna Abdulaziz Musa a wuya, wanda a yanzu yake jinya a asibiti.