’Yan sanda na zaluntarmu – Mutanen Nguroje
Al’ummar garin Nguroje da ke karamar Hukumar Sardauna a Jihar Taraba sun bukaci Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ya dauki mataki kan yadda ’yan sanda ke kafa shingayen duba ababen hawa a jihar suna zaluntarsu. Mai magana da yawun al’ummar garin Nguroje Malam Yakubu Isma’ila ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa […]
Al’ummar garin Nguroje da ke karamar Hukumar Sardauna a Jihar Taraba sun bukaci Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ya dauki mataki kan yadda ’yan sanda ke kafa shingayen duba ababen hawa a jihar suna zaluntarsu.
Mai magana da yawun al’ummar garin Nguroje Malam Yakubu Isma’ila ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Jalingo. Ya ce kiran ya zama tilas ganin yadda jami’an tsaro ke takura wa jama’a musamman a ranakun kasuwa.
Ya ce kwanan nan wasu ’yan sanda suka kashe wasu matasa uku a garin Nguroje don kawai sun ki tsayawa su ba su cin hanci.
MalamYakubu Isma’ila ya ce abin da ya faru shi ne a ranar kasuwar Nguroje ’yan sanda suka tsayar da matasan da ke kan babur don su karbi kudi a hannunsu amma matasan suka ki tsayawa, sai ’yan sandan suka tayar da motarsu kirar Hilud Toyota suka bi matasan suka banke su da motarsu inda biyu suka mutu nan take na ukunsu ya mutu kwana daya daga bisani. Ya ce wannan lamari ya tunzura matasa suka nemi daukar fansa amma manyan gari suka hana.
Malam Isma’ila ya ce abin da ya daure wa jama’ar garin kai shi ne duk da cewa an kai kara ga hukuma kan wannan lamari, har yanzu ba wani mataki da ta dauka.
Ya ce a duk ranakun kasuwa a daukacin fadin jihar, ’yan sanda da sojoji da sauran jami’an tsaro na kafa shingaye daban-daban suna karbar kudi da karfi a hannun talakawa, kuma duk wanda ya ki bayar da kudi komai gaskiyarsa zai fuskanci wulakanci a hannunsu kuma ba inda zai kai kara.
Ya ce suna son Sufeto Janar din da gwamnatin Jihar Taraba su binciki lamarin don a hukunta ’yan sandan da suka kashe matasan uku kuma a biya iyalansu diyya.
Binciken Aminiya ya gano ana kafa shingaye fiye da takwas a kowane bangaren shiga manyan kasuwanni jihar a ranakun da kasuwa ke ci, kamar kasuwar Iwareda da kasuwar Ladi da ta Garba Chede da ta Mutum Biyu da Tella da Bali da Maihula da Nguroje da sauransu, kuma ana karbar kudi daga hannun masu motocin haya da ’yan acaba.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Taraba, Ademola Omole ya tabbatar da aukuwar lamarin garin Nguroje kuma ya ce ana gudanar da bincike don gano gaskiyar batun.