’Yan sanda sun ƙwace sakamakon zaɓe a Ribas

Masu jefa ƙuri’a da ma’aikatan hukumar sun tsere don tsira da rayukansu.

’Yan sanda sun ƙwace sakamakon zaɓe a Ribas

Ma’aikatan Hukumar Zaben Jihar Ribas (RSIEC) da masu jefa ƙuri’a a Makarantar Firamare ta Elekahia, sun tsere biyo bayan da wata raraka da jami’an ’yan sanda suka kai.

Kimanin motoci 21 ƙirar Hilux ɗauke da jami’an ’yan sanda ne suka isa makarantar da ke da rumfunan zaɓe guda 10.

Jami’an RSIEC da suka kammala gudanar da zaɓen, sun bar wajen bayan da jami’an suka ƙwace wasu takardun zaɓen.

Wasu daga cikin ’yan sandan da suka rufe fuskokinsu sun umarci jami’an RSIEC da su cire rigunansu na aiki.

Daga bisani jami’an suka harba barkonon tsohuwa, wanda hakan ya sa mutane suka fara gudu don tsira da rayukansu.

Yawancin jami’an RSIEC da masu jefa ƙuri’a sun tsere, lamarin da ya haifar da tashin hankali a yankin.

Motocin ’yan sandan sun yi saurin ficewa daga wajen tare da kayan zaɓe da dama.

Sai dai kakakin rundunar ’yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta ce ba ta da masaniya, kan lamarin.

Tun da farko, Sufeto-Janar na ’Yan Sanda (IGP), Kayode Egbetokun, ya umarci jami’ansa da kada su bayar da tsaro a yayin zaɓen, biyo bayan wani umarnin kotu.

Sai dai umarnin ma Sufeton ’yan sandan ya haifar da ruɗani, lamarin da ya sanya cacar-baki tsakaninsa da gwamnan Jihar Ribas, Fubara.

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025