’Yan sanda sun bankado wurin kyankyashe jarirai 2 a Ribas
Ana zargin wata mata da zama shugaban ma’aikatar da ake sayar sa jariran.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta gano wuraren kyankyashe jarirai guda biyu a yankunan Igwuruta da Omagwa a jihar.
Sanarwa da kakakin rundunar, Grace Iringe-Koko, ya fitar a ranar Talata, ta ce rundunar ta ceto mata 10 masu ciki daga wuraren kyankyasar jariran.
- Hajjin 2023: An bukaci maniyyatan Abuja su fara biyan N2.5m
- Wata daya kafin zabe, Kotu ta haramta wa Elisha Abbo takarar Sanata a APC
“An cafke wata mata da ake zargin ita ce shugaba, idan matan sun haihu tana karbar jariran ta ba su kudi dubu N500.
“Akwai mutum uku da aka cafke tare da matar, maza biyu da mace daya.”
Kakakin ya ce sun kwato mota kirar Honda Jeep a hannun wadanda ake zargin, wadda da ita suke jigilar masu cikin.
Kazalika, ya ce rundunar na bincike don gano mutumin da yake sayen jariran.