’Yan sanda sun binciki kantin kasar Sin mai lakabin ISIS

Wani kantin an yi masa lakabin sunan ’yan tada kayar baya na ISIS, al’amarin da ya bai wa mutane mamaki shi ne bai dauki hankalin al’umma ba, amma ya jawo hankalin ’yan sanda.’Yan sanda sun fara binciken wannan kantin sayar da suturun alfarma na ISIS.Wannan suna na ISIS ya shahara ne a wajen ’yan tayar […]

’Yan sanda sun binciki kantin kasar Sin mai lakabin ISIS
’Yan sanda sun binciki kantin kasar Sin mai lakabin ISIS

Wani kantin an yi masa lakabin sunan ’yan tada kayar baya na ISIS, al’amarin da ya bai wa mutane mamaki shi ne bai dauki hankalin al’umma ba, amma ya jawo hankalin ’yan sanda.
’Yan sanda sun fara binciken wannan kantin sayar da suturun alfarma na ISIS.
Wannan suna na ISIS ya shahara ne a wajen ’yan tayar da kayar bya da ta’addanci da ke kai hare-hare a kasashe, wadanda suka hada da na kasashen Lebanon da Faransa.
Ita kuwa mai wannan kanti na sayar da  suturun kawa, mai suna Chen, ta bayyana wa ’yan sanda cewa, ta yi amfani da lakabin ne na “ISIS,” saboda ma’anarsa a harshen Mandarin da ake furtawa a matsayin “is-is,” amma ainihin furucin shi ne “yisi-yisi,” kalmar da ke da ma’anar aikewa da sakonnin kyaututtuka ga mutum don nuna godiya.
Chen ta bude wannan shago ne tun a shekarar 2012, inda ta shahara wajen sayar da suturun mata na alfarma.
Ba a jima da ’yan sanda suka kai mata sammaci ne sai Chen ta cire wannan lakanin suna mai haruffa hudu, duk da cewa, binciken ’yan sandan ya wanke ta daga duk wata alaka da kungiyar ’yan ta’adda.