‘Yan sanda sun bukaci jam’iyyu da yin kamfen cikin lumana

Hukumar ‘yan sandan jihar Benuwe sun bayyana wa jam’iyyun siyasa da su nemi izinin fara yin kamfen akalla sa’o’i 48 kafin a fara gudanar da harkokin siyasa. Kwamishinan ‘yan sanda jihar Benuwe Ene Okon, ne ya sanar da hakan a Makurdi lokacin da suke ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyun wanda aka yi […]

‘Yan sanda sun bukaci jam’iyyu da yin kamfen cikin lumana

Hukumar ‘yan sandan jihar Benuwe sun bayyana wa jam’iyyun siyasa da su nemi izinin fara yin kamfen akalla sa’o’i 48 kafin a fara gudanar da harkokin siyasa.

Kwamishinan ‘yan sanda jihar Benuwe Ene Okon, ne ya sanar da hakan a Makurdi lokacin da suke ganawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyun wanda aka yi tare da ‘yan sanda.

Okon, ya bukaci duk jam’iyyun kasar da su gudanar kamfen cikin lumana don samun nasarar zaben 2019.