’Yan sanda sun cafke ƙasurgumin ɗan fashi da makami a Kano
Rundunar ta cafke ɗan fashin yayin da yake ƙoƙarin tserewa a kan babur.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, ta sanar da cafke wani ƙasurgumin ɗan fashi da makami tare da ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda biyu da kum alburusai 47.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce sun kuma samu kuɗi kimanin Naira miliyan 4.9 a hannun wanda ake zargin.
- Muna neman masu daukar nauyin zanga-zanga ruwa a jallo —Gwamnati
- An aike masu zanga-zanga 632 gidan yari a Kano
A ranar Litinin da misalin ƙarfe 2 na dare ne, wani mazaunin garin Yandadi a ƙaramar hukumar Kunchi da ke Jihar Kano, ya kai rahoton cewa ’yan fashi sun kai masa hari a gidansa, sannan kwashe masa kuɗi Naira miliyan 15.
Duk da tarzomar da ake fama da ita a Kano sakamakon zanga-zangar yunwa, kwamishinan ’yan sandan jihar, Salman Dogo Garba, ya bayar da umarnin bin sahun waɗanda suka aikata laifin.
Da misalin ƙarfe 6 na safiyar ranar Talata ne, ‘yan sanda suka kama ƙasurgumin ɗan fashin mai suna Hassan Iliya, mai shekara 35 mazaunin garin Alhazawa a ƙaramar hukumar Musawa ta Jihar Katsina.
Ya shiga hannun rundunar ne yayin da yake ƙoƙarin tserewa a kan babur.
An samu bindiga ƙirar AK-47 guda biyu tare alburusai 47 da kuma kuɗi har N4,986,000.00 a cikin wata jakarsa.
Rundunar ta ce a yanzu haka tana ci gaba da gudanar da bincike.