’Yan sanda sun cafke ɓata gari 96 a Abuja
Kwamishinan ya ce an kama ɓata garin ne a sassa daban-daban na Abuja.
Jami’an Rundunar ’Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja, sun cafke ɓata gari 96 da ake zargi da laifin fashi da makami.
Kwamishinan ’yan sandan babban birnin tarayya Abuja, CP Benneth Igweh, yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a ranar Talata, ya ce an kama su ne a yankunan Nyanya, Galadimawa, Kubwa, Kabusa, Lubge, Mabushi, Iddu, Karmo da Byazhin.
- Kwalara ta kashe mutane 63, wasu 2,102 sun kamu —NCDC
- DAGA LARABA: Digiri Ko Sana’a —Wanne Ya Fi Muhimmanci?
Ya ƙara da cewa samamen da suka kai lokaci guda a ranar Litinin, sun haɗa da yankunan Asokoro, Jikoyi da kuma Karshi.
Ya ce abubuwan da suka gano a lokacin samamen sun haɗa da wuƙaƙe, almakashi guda biyu, tukunyar gas, na’urar hasken rana, guduma da katunan shaida.
Ya ƙara da cewar za a gurfanar da su gaban kotu.
CP Igweh, ya ƙara da cewa, jami’an rundunar da ke Durumi sun ƙwato wata mota ƙirar Peugeot mai lamba: BWR 855 AS, wacce wasu ’yan bindiga suka sace a kusa da Wuse, shiyya ta 3, bayan sun yi tsere sun barta a kusa da gidan mai na Conoil Filling, da ke Durumi.
Har wa yau, ya ƙara da cewa, “Kuma yayin da ake bincike, an gano motar na ɗauke da bayanan Meshach Osayende da ke rukunin gidaje na BUH a Kado tare da lambar waya.”