’Yan sanda sun cafke barayi 11 a Jigawa

Rundunar ta ce za a gurfanar da su a gaban kuliya da zarar an kammala bincike a kan su.

’Yan sanda sun cafke barayi 11 a Jigawa

Wasu ’yan sandan Najeriya a bakin aiki

Rundunar ’yan sandan Jihar Jigawa, ta cafke wasu mutum 11 da ake zargi da satar dabbobi, mota, babura da sauran kayayyaki a wasu kananan hukumomin jihar uku.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Laraba a Dutse cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wurare daban-daban tsakanin a kananan hukumomin Babura, Kiyawa da Suletankarkar.

Shiisu, ya ce daya daga cikin wadanda ake zargin mai shekara 25 daga garin Gujungu, an kama shi ne da shanu biyu da ake zargin na sata ne a hanyar Kiyawa zuwa Balago.

Jami’in ya ce a yayin bincike, wanda ake zargin ya kasa yin gamsasshen bayani kan shanun.

An kuma kama wani mai shekara 22, mazaunin Bakin Kasuwa a Kiyawa, wanda ake zargi da sace wasu kwanon rufi 15, ya amsa cewa sato kwanon ya yi a wani gida da ke yankin.

Akwai wasu mutum biyu kuma; daga kauyen Makale Insharuwa da kuma kauyen Dugujabe a Karamar Hukumar Babura an kama su bisa zargin satar babur, kuma sun amsa laifin.

A cewarsa, an kama wasu shida kan zargin satar tumaki da awaki da janareta a Karamar Hukumar Kazaure, cikinsu har da da wani mai shekara 25 dan Jamhuriyar Nijar.

Sai dai, ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan wadanda ake zargin, da zarar an kammala za a mika su zuwa kotu.

’Yan Bindiga: An miƙa wa gwamnatin Kaduna mutum 58 da aka ceto

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7

Hajjin 2025: Maniyyata za su fara ajiye N8.4m a Kaduna

Barikin Ladi: Asalin garin da yanayin rayuwar mazauna