’Yan sanda sun cafke mace mai garkuwa da mutane a Kano

An gano cewa matar ce shugabar gungun masu garkuwa da mutanen

’Yan sanda sun cafke mace mai garkuwa da mutane a Kano

’Yan sandan sun kama wata mata da wasu maza biyu da suka yi garkuwa da dan mai unguwar Galadanchi, Ado Sunusi a Karamar Hukumar Gwale, Jihar Kano.

Bayan ’yan sanda sun zurfafa bincike, sun gano motar da aka sace yaron, suka kuma kamo direban motar a titin Beruit, cikin birnin Kano.

Ta hanyarsa ne aka gano maboyar matar wadda ita ce shugabar gungun masu garkuwar da mutanen tare da wasu daga cikin yaranta.

Rundunar ’Yan Sandan Kano, ta bayyana cewa ta cika hannu da mutanen ne a samamen da jami’anta suka kai maboyar masu garkuar da ke a Unguwar Jaba da ke karamar hukumar Ungogo.

Ta ce matar da maza uku ne aka kama a gidan, amma biyu daga cikin mazan an tabbatar da ’yan asalin Jihar Zamfara ne.

Bincike ya nuna cewa matar ta kama hayar gidan da suke zaune a Unguar Jaba ne kan N600,000 duk shekara a hannun wani dilalli.

Matar ta fada wa ’yan sanda cewa ta fara garkuwa da mutane ne bayan  an kashe mijinta a Jihar Zamfara.

Matashi ya shiga hannu kan safarar tabar wiwi

Na yi shekara 20 ina fim amma har yanzu ina fama da talauci — Djimon Hounsou

Tinubu ya tafi Abu Dhabi taro

Lakurawa sun kashe ma’aikatan Airtel 3 a Kebbi