Yan sanda sun cafke masu safarar yara a Kano

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta cafke wasu ma’aurata da kuma wata ma’aikaciyyar jinya bisa zarginsu da hadin baki tare da yunkurin safarar wani yaro. Aminiya ta kalato cewa wacce ake zargin mai suna Misis Itohan Pius, wacce ma’aikaciyar Asibitin Ido na ECWA da ke Kano ce, an kuma samu rahoton cewa ba wannan […]

Yan sanda sun cafke masu safarar yara a Kano

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta cafke wasu ma’aurata da kuma wata ma’aikaciyyar jinya bisa zarginsu da hadin baki tare da yunkurin safarar wani yaro.

Aminiya ta kalato cewa wacce ake zargin mai suna Misis Itohan Pius, wacce ma’aikaciyar Asibitin Ido na ECWA da ke Kano ce, an kuma samu rahoton cewa ba wannan ne karo na farko da aka taba samunta da wannan laifin ba, domin ko a kwanakin baya wasu mutane sun taba kama ta

tana kokarin satar jariri; inda har suka yi mata dukan kawo wuka.

Da take bayyana yadda abin ya faru, Misis Itohan Pius ta bayyana cewa wata karuwa ce da ke zaune a Unguwar Sabon Gari ta yi mata alkawari za ta kawo mata yaron da za ta ba ma’auratan. “Da ma akwai wata mata da ta ce za ta kawo mani yaro, don haka lokacin da wadannan ma’aurata suka zo suka gaya mani bukatarsu cewa suna son yaro namiji, wanda bai wuce watanni biyar da haihuwa ba; kasancewar sun yi aure shekara tara amma ba su haihu ba, sai na je na wajen wannan mata a Sabon Gari na karbo masu yaron a wurinta. Ni ban taba aikata irin wannan abu ba, tsautsayi ne,” inji ta.

Tun da farko ma’auratan Mista da Misis Charles Mpaka Bob Manuel, wadanda mazauna garin Akulga a karamar Hukumar Akuku-Toru a Jihar Ribas ne, sun zo Jihar Kano ne musamman don sayen yaro, inda a cewarsu saboda sun kwashe tsawon shekara tara da aure ba tare da sun taba haihuwa ba.

Ita ma mahaifiyar yaron wacce ake zargi da cefanar da dan nata mai suna Zainab, ta yi karin haske game da yadda ta karbi Naira dubu 13 a matsayin kafin alkalami daga cikin Naira dubu 20 kudin fansar da wannan da nata, wanda ake zargin ta haife shi ba cikin aure ba. “Daman ni tun farko ban yi niyyar sayar da yarona ba, na amince mata ne don a samu hanyar da ’yan sanda za su kama ta,” inji ta.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano DSP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar wannan al’amari, ya kuma lashi takobin cewa da zarar bincikensu ya kammala, za su gurfanar da su gaban kuliya. “Kimanin tsawon shekaru biyu ke nan Jihar Kano na fama da satar yara, musamman a unguwannin Hotoro da Kawo, don haka rundunarmu ba za ta yi wasa da al’amarin ba har sai ta ga wadanda ake zargin sun fuskanci hukunci.”

Majiya ya kara da cewa, “uwar yaron ce ta sanar da jami’anmu kan lamarin, inda aka shirya wa ita ma’ikaciyar asibitin ECWA kofar raggo, har a karshe aka kai ga kama ta. Wani abin mamaki shi ne, kafin zuwan ’yan sanda wurin, ita wacce ake zargin har ta yi amfani da karfi don kwace yaron daga hannun uwarsa, sai dai burinta bai cika ba, inda a karshe ga ta nan a hannunmu. ”

Sai Asibitin ECWA ya nisanta kansa daga aika-aikar da ma’aikaciyarsu ta aikata, inda ake zarginta da hannu cikin harkar saye da sayar da yara, wanda laifi ne da ya saba dokokin kasar nan.

A cikin takardar da Shugaban Asibitin Ido na ECWA, Dokta Atima O. Mayor, ya bayyana cewa hukumar asibitin na jan hankalin jama’a da su fahimci cewa laifin da Madam Itohan ta aikata, ta aikata shi ne bisa radin kanta, domin ya ci karo da tsari da dokokin da aka kafa asibitin a kansu.

A cewar takardar, tun daga lokacin da wannan al’amari ya faru asibitin ya dauki matakin korar ma’aikaciyar bisa bata sunan asibitin da ta yi a wajen al’umma.