’Yan sanda sun cafke matasa 7 da makamai da layu 582 a Gombe

’Yan sanda sun kama matasa bakwai kan laifin yin sojan gona da kuma layu 582 a garin Kaltungo a jihar Gombe

’Yan sanda sun cafke matasa 7 da makamai da layu 582 a Gombe

’Yan sanda sun kama wasu matasa bakwai kan laifin yin sojan gona da kuma layu 582, a garin Kaltungo a jihar Gombe

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mahid Mu’azu Abubakar, ya ce dubun waɗanda ake zargin ta cika ne inda aka kama su da makamai da tabar wiwi da tulin kwayoyi daban-daban.

Ya ce an kama matasan, masu shekaru 17 zuwa 21 ne a wani samame da ’yan sanda suka kai wata maboya a kasuwar garin Kalarin da Baganje a Karamar Hukumar Kaltungo, a ranar 3 ga watan Disamba 2023.

Ya ce abubuwan da aka a wajen su a matsayin kayan shaida sun hada kakin soja guda daya da hula hana-sallah, gidan harsashin bindiga kirar AK 47, da takubba da wukake da kuma gatari.

Sauran sun hada wukake da kwayar exzol, kulli 19 na tabar wiwi, kati 40 na kwayar Tramadol, layu guda 582, da kuma wata riga da aka dinka ta da layu.

Daga nan sai ya ce akwai sauran matasan da zargin, wadanda rundunar ke ci gaba da kokarin kamo su domin fuskantar shari’a.

Babban layin wutar lantarki ya faɗi karon farko a 2025

Na yi nadamar yi wa Tinubu kamfe a 2023 — Ɗan Bilki Kwamanda

Yadda na ƙi karɓar cin hancin N5bn a gwamnatin Tinubu – Tsohon Hadimi

Zulum ya bai wa sabon Shehun Bama sandar sarauta