’Yan sanda sun cafke mutum 8 kan sata da miyagun laifuka a Yobe

Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike a kansu kafin gurfanar da su a gaban kotu.

’Yan sanda sun cafke mutum 8 kan sata da miyagun laifuka a Yobe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Yobe, ta kama mutum takwas da ake zargi da hannu a laifukan sata, hare-hare da kuma miyagun laifuka a sassa daban-daban na jihar.

Kakakin rundunar, SP Dungus Abdulkarim, ya ce an kama mutanen ne a wasu samame da jami’an tsaro suka kai a Ƙananan Hukumomin Bursari, Damaturu da Nguru.

Ya ƙara da cewa an kuma ƙwato wasu kayayyakin da ake zargin na sata ne, ciki har da babur.

A Bursari, jami’an ’yan sanda sun kama wani matashi mai suna Musa Musa mai shekara 25 bisa zargin satar kayan ginin da aka tanada domin gyaran Makarantar Firamare ta Daskum.

An ce an kama shi ne yayin da yake jigilar kayan a kan hanyar Gashua.

Haka kuma an ƙwato wani babur da ake zargin an yi amfani da shi wajen aikata laifin, yayin da wani da suke aikata laifin ya tsere.

A Damaturu kuwa, ’yan sanda sun kama wasu matasa biyu, Adam Maigaimu mai shekara 20 da Mohammed Umar mai shekara 18, sakamakon yin faɗa da gatari tare da jikkata wasu mutane.

Ana kuma zarginsu da satar rago da sayar da shi domin amfanin kansu.

Hakazalika, jami’an rundunar Nguru sun kai samame wata maɓoya da ake zargin masu laifi na amfani da ita a Anguwar Yan Rake, inda suka kama wasu mutane biyar.

Rundunar ta ce tana ci gaba da bincike a kansu, yayin da ake ƙoƙarin kamo sauran mutanen da ake zargi da hannu a laifukan.