’Yan sanda sun cafke ‘sojan gona’ a Kano

Sojan gonar ya shiga hannun lokacin da ya ke kokarin damfarar wani mai adaidaita sahu.

’Yan sanda sun cafke ‘sojan gona’ a Kano

‘Yan sanda yayin kamen wani mai laifi

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta cafke wani sojan gona wanda ya kware wajen karbar na goro a hannun matuka babur din A Daidaita Sahu.

Kakakin ’yan sandan Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata cewa sh dai wannan sojan gona dubunsa ta cika ne wa wani caji ofis da ya kai kara.

Ya ce wanda ake zargin mai suna Abubakar Zailani Ibrahim, mai shekara 27 , ya kama wani matukin A Daidaita Sahu tare da kai shi ofishin ’yan sanda na Rijiyar Zaki da ke Kano.

Ya ce “Wanda ake zargin ya yi karar matukin babur din ne cewa ya taba tsere masa da kakinsa na aikin soja da kuma wasu kayan kudi na kimamin N195,000.”

Majiya ya ce bayan nan ne Kwamishinan ’Yan Sandan jihar ya ba wa baturen ’yan sandan caji ofis din Rijiyar Zaki damar gudanar da bincike.

A cewarsa, bayan gudanar da bincike ne aka gano cewa wanda ake zargin ba soja ba ne kuma karar da ya ke yi ba gaskiya ba ce.

“Bayan zurfafa bincike wanda ake zargin uya bayyana cewa ba jami’in soja bane, kuma wannan ita ce hanyar da ya kware wajen damfarar matuka babur din A Daidaita Sahu a jihar.

“Ya kara da cewa daga Adamawa ya zo Kano saboda ya dinga aikata irin wannan laifi.”

Kiyawa ya kuma bayyana cewa rundunar ’yan sandan jihar za ta ci gaba da bincike kan lamarin don gano masu suke aikata irin wannan danyen aiki.