‘Yan sanda sun cafke sojan gona a Legas
Sojan gonan ya kware wajen aikata laifuka ta hanyar amfani da kakin sojoji.
Rundunar ’Yan Sandan jihar Legas, ta kama wani sojan gona wanda sojoji ke nema ruwa a jallo a jihar.
Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin ne, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Asabar.
- Mahaifin tsohuwar jarumar Kannywood Muhibbat Abdussalam ya rasu
- Ramadan: Gidauniyar Dangote ta raba buhunan shinkafa miliyan ɗaya a bana
Hundeyin, ya ce an kama wanda ake zargin ne lokacin wani samame da rundunar ta kai rukunin gidaje na Fagbile.
Ya ce rundunar sojan gonan da ya kware wajen amfani da kakin soja, inda yake aikata munanan laifuka.
“Ba tare da bata lokaci ba muka aika a kira Kwamandan dakarun soji domin tafiya da wanda ake zargin.
“Sojoji sun tabbatar da cewa sojan gona ne. A yayin da ake yi masa tambayoyi, wanda ake zargin ya tabbatar da cewar shi ba sojan gaske ba ne.
“Sojoji sun tabbatar da cewa yana cikin wanda suke nema ruwa a jallo. Za a gurfanar da shi a kotu da zarar an kammala bincike,” in ji shi.