’Yan sanda sun cafke ’yan bindiga ɗauke da makamin roka a Yobe

Masu yi wa ’yan bindiga safarar makaman roka sun shiga hannun ’yan sanda a Yobe

’Yan sanda sun cafke ’yan bindiga ɗauke da makamin roka a Yobe

’Yan sandan a yankin Karasuwa na Jihar Yobe sun cafke wasu da ake zargin ’yan bindiga ne, dauke da makamin roka, wanda aka fi sani da RPMG Motar.

Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Dungus Abdulkarim ya bayyana mutane biyun da aka kama sun shigo Jihar Yobe ne daga Zamfara.

Dungus ya ce, “na farko da aka kama ne ya bayyana cewa dayan ne mai yin safarar makamai ga ’yan ta’adda a Zamfara, shi ne ’yan sanda suka bi sawunsa har yankin Maradun a Jihar ta Zamfara suka kamo shi, ana kuma ci gaba da binciken wadanda ake zargin.

“An kama wanda ake zargin na farko yana tuka mota Toyota Hiace mai dauker mutum 18 a Karasuwa, sakamakon rahoton sirri da aka samu a lokacin da yake kokarin karbar wannan makami na roka (RPMG),” in ji sanarwar da jami’in ya fitar.

Dungus ya ce bincikensu ya gano wadanda ake zargin suna kai wa ’yan bindiga makamai ne a jihohin Zamfara, Kano, Neja, Kaduna, Yobe da dai sauransu.

Ya kara da cewa Kwamishanan ’yan sandan jihar, Garba Ahmed ya yi alkawarin ci gaba da  karfafa gwiwar jami’an runduar gwiwa domin ci gaba da zakulo ’yan ta’adda da kuma yin maganin su.

Ya shawarci jama’a da su ci gaba da baiwa ’yan sanda bayanai masu amfani da zai kai ga damke masu laifin da ke cikin al’umma.