’Yan Sanda sun cafke ’yan fashi a Gombe

Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe sun cafke wasu mutane biyu da suka addabi yankin Kuri da Lamban a karamar Hukumar Yamaltu da fashi da makami.Da yake gabatar da ’yan fashin ga manema labarai a hedikwatarsu, Kwamishinan ’yan sandan jihar, Abdullahi Kudu Nma ya ce sun kama mutanen ne a yankin karamar Hukumar Yamaltu Deba da […]

’Yan Sanda sun cafke ’yan fashi a Gombe
’Yan Sanda sun cafke ’yan fashi a Gombe

Rundunar ’yan sandan Jihar Gombe sun cafke wasu mutane biyu da suka addabi yankin Kuri da Lamban a karamar Hukumar Yamaltu da fashi da makami.
Da yake gabatar da ’yan fashin ga manema labarai a hedikwatarsu, Kwamishinan ’yan sandan jihar, Abdullahi Kudu Nma ya ce sun kama mutanen ne a yankin karamar Hukumar Yamaltu Deba da kananan bindigogi biyu kirar hannu da kuma adduna da wukake.
Ya bayyana cewa su ne ke tare hanyar kasuwannin kauyuka na tsakanin wadannan garuruwa suna yi wa mutane fashi.
Abdullahi Alhaji, daya daga cikin ’yan fashin ya tabbatar wa wakilinmu cewa yana aikata fashin amma wasu abokansa ne suka sa shi a harkar. Ya ce ba su kashe mutum sai dai su karbi kudinsa ko kayansa. “Na karbi dubu talatin a hannun wani a garin Kuri, a lokacin da muka shiga gidansa sannan kuma na karbi wasu dubu arba’in a wani karon a hannun wani mutum a garin Lamban amma ban taba kashe wani ba,” inji shi.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi