’Yan sanda sun ceci matafiya 20 daga hannun ’yan ta’adda a Katsina
Matafiya 20 sun tsallake rijiya a hannun ’yan bindiga da suka kai wa motocin hayan da suke ciki hari a Jihar Katsina
Matafiya 20 sun tsallake rijiya a hannun ’yan bindiga da suka kai musu hari a kananan hukumomin Jibia da Faskari a Jihar Katsina.
Rundunar ’yan sandan jihar ta ce jami’anta ne suka kubutar da rukunin farko a matafiyan su 10, da ’yan ta’addan suka kai wa farmaki a yankin Kwanar Makera da ke hanyar Katsian zuwa Magamar Jibia a Kamar Hukumar Jibia a ranar Asabar.
Kakakin Runduanar, Abubakar Aliyu, ya bayyana cewa kafin maharan su kai ga sace matafiyan ne jami’an rundunar suka kai dauki suka ragargaje su, inda suka cika bujensu da iska, wasu daga cikinsu da raunin harbi.
Ya ce hari na biyu jkuma an kai shi ne a yankin Marabar Bangori da ka kan hanyar Funtuwa zuwa Gusau a Karamar Hukumar Faskara, inda ’yan bindiga suka yi wa wata motar haya dauke da fasinjoji 10 kwanton bauna, amma kafin hakarsu ta cim ma ruwa jami’an suka fatattake su, suka kubutar da mutanen