‘Yan sanda sun ceto dillalin shanu da aka sace a Edo

Rundunar ta ce amfani da jirage ya taimaka mata wajen ceto wanda aka sace.

‘Yan sanda sun ceto dillalin shanu da aka sace a Edo

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Edo, sun ceto wani dillalin shanu, mai suna Peter Balogu, wanda wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne suka sace shi.

Rundunar ta ce an yi garkuwa da Balogun ne a ranar 7 ga watan Yuli, 2026, a kan hanyar Igarra zuwa Auchi.

An ceto shi a ranar 15 ga watan Yuli bayan wani samamen da jami’an tsaro suka kai yankin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Eno Ikoedem, ta ce jami’an Sashen Yaƙi da Garkuwa da Mutane, Sashen Yaƙi da Manyan Laifuka (VCRU) da kuma Sashen Amfani da Jiragen Sama Marasa Matuƙa ne suka gudanar da aikin ceto.

Ta bayyana cewa jami’an tsaron sun gudanar da bincike a cikin Dajin Imoga da sauran yankuna, inda suka yi amfani da bayanan sirri, jiragen sama marasa matuƙa da kuma jirgin sama mai saukar ungulu.

Ta ce da masu garkuwar suka hangi jirgin saman ‘yan sanda, sai suka firgita, suka bar wanda suka sace, sannan suka tsere zuwa cikin dajin.

A cewarta, matsin lambar da jami’an tsaro suka ci gaba da yi, tare da sa ido ta jiragen sama marasa matuƙa da jirgi sama mai saukar ungulu, ya tilasta wa masu garkuwar guduwa.

Balogun, ya shaida wa ‘yan sanda cewa yawan sintirin jirgin sama mai saukar ungulu ne ya tsorata masu garkuwar, wanda hakan ya sa suka bar shi suka gudu.

Rundunar ‘yan sandan ta ce an riga an miƙa Balogun ga iyalansa.