’Yan sanda sun ceto mutum 23 da aka sace a Kaduna
Rundunar ta ce za ta ci gaba da yaƙi da ta’addanci a faɗin jihar.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, tare da Sojoji sun samu nasarar ceto mutum 23 da ’yan bindiga suka sace a wani artabu da aka yi a ƙauyen Doka, da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, DSP Mansur Hassan, ya fitar, ya bayyana cewa babban jami’in ’Yan Sandan yankin Kajuru ne ya jagoranci samamen.
Ya ce bayan samun bayanan sirri game da maharan, jami’an tsaro sun kai farmaki inda suka ceto dukkanin mutanen 23, waɗanda mazauna Kauru ne.
A yayin artabun, wasu daga cikin maharan sun mutu, yayin da wasu suka tsere cikin daji da raunukan harbin bindiga.
A cewar sanarwar, an sake haɗa mutanen da iyalansu a Ƙaramar Hukumar Kauru.
An luma ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin domin tabbatar da cewa babu wata fargaba.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Rabiu Muhammad, ya bayyana gamsuwarsa da wannan gagarumar nasarar.
Ya ce za su ci gaba da yaƙi da ta’addanci a Jihar Kaduna bisa jagorancin Gwamnan Jihar, Uba Sani.