’Yan sanda sun ceto mutum 9 daga hannun masu garkuwa a Kaduna

’Yan sanda biyu sun rasa rayukansu bayan ’yan bindigar sun yi musu kwanton ɓauna yayin da suke dawowa daga aikin ceto.

’Yan sanda sun ceto mutum 9 daga hannun masu garkuwa a Kaduna

Jami’an tsaro sun ceto mutum tara da aka yi garkuwa da su bayan wani samame da ya tilasta wa ’yan bindiga tserewa su bar waɗanda suka sace a daji a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Sai dai ’yan sanda biyu sun rasa rayukansu bayan da ’yan bindigar suka yi musu kwanton ɓauna yayin da suke dawowa daga aikin ceto.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da kakakinta, DSP Mansir Hassan, ya fitar a ranar Alhamis.

Sanarwar ta ce an yi garkuwa da mutanen ne a ranar Laraba daga gonakinsu da ke kusa da ƙauyen Unguwan Sa’idu, wanda ke kusa da garin Birnin Gwari.

A cewar rundunar, bayanan sirri da aka samu da misalin ƙarfe 12:45 na rana sun nuna cewa kimanin ’yan bindiga 15 ɗauke da muggan makamai na aiki a yankin, kuma sun yi garkuwa da mutane da dama.

Bayan samun rahoton, kwamanda da DPO na Yankin Birnin Gwari suka tattara jami’an sintiri da suka haɗa da na ’yan sandan kwantar da tarzoma da jami’an sintiri na Jihar Kaduna (KADVIS), inda suka nufi wurin domin ceto waɗanda aka sace.

Da isarsu wurin sun yi artabu da ’yan bindigar, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa cikin daji a kan babura.

“Jami’an sun ci gaba da bin su ba tare da sassautawa ba, lamarin da ya tilasta wa maharan barin waɗanda suka yi garkuwa da su tare da tserewa domin tsira da rayukansu,” in ji sanarwar.

Waɗanda aka ceto sun haɗa da Hudu Rabiu mai shekara 31, Yusuf Sagir mai shekara 20, Sagir Rabiu mai shekara 17, Muhammad Kabir mai shekara 23, Kabir Lawal mai shekara 20, Idris Abubakar mai shekara 17, Mustapha Zayyanu mai shekara 18, Kabiru Rabiu mai shekara 18 da Usman Lawal mai shekara 18.

Rundunar ta ce an tarar da mutanen da aka yi garkuwa da su ɗaure da igiyoyi bayan masu garkuwa da su sun gudu. Daga bisani an ceto su lafiya kuma aka haɗa su da iyalansu.

Sai dai rundunar ta ce abin takaici ya faru ne yayin da jami’an tsaron ke dawowa daga aikin.

Ta yi zargin ’yan bindigar da suka tsere sun yi wa jami’an kwanton ɓauna a hanya, inda suka buɗe musu wuta, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar jami’an ’yan sanda biyu bayan sun samu munanan raunukan harbin bindiga.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Rabiu Muhammad, ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalai da abokai da kuma abokan aikin jami’an da suka rasu.

Ya bayyana sadaukarwar tasu a matsayin wata shaida ta jarumtaka da ƙwazo da kuma sadaukar da kai da jami’an tsaro ke yi a kullum wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.

Kwamishinan ya ce rundunar za ta ci gaba da girmama tunawa da jami’an da suka rasu, tare da ci gaba da ƙoƙarin yaƙi da matsalar rashin tsaro a faɗin jihar.

Ya ƙara da cewa bincike da kuma wasu matakan tsaro na musamman na ci gaba domin gano maharan tare da gurfanar da su a gaban doka.