’Yan sanda sun ceto yara 4 da aka sace daga Bauchi a Anambra

‘Yan sandan sun gano yaran ne bayan an sayarwa wasu mutane a Jihar Anambra.

’Yan sanda sun ceto yara 4 da aka sace daga Bauchi a Anambra

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Anambra, ta ceto wasu yara huɗu da aka sace a Jihar Bauchi, sannan aka sayarwa wasu mutane a Jihar Anambra.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Obono Itam ne, ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin wata tattaunawa da manema labarai a Awka.

An kama mutum huɗu, ciki har da wata mata da ta karɓi yaran ba bisa ƙa’ida ba.

Waɗanda ake zargin sun amsa laifinsu, kuma ana ƙoƙarin haɗa yaran da iyayensu.

A wani harin haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka kai a ranar 24 ga watan Disamban 2024, sun lalata sansanin ’yan ta’adda a ƙauyen Nimo da ke Ƙaramar Hukumar Njikoka.

A yayin wannan samame, jami’an sun gano abubuwa masu fashewa guda 19.

Hakazalika, jami’an sun rushe gine-ginen da ’yan ta’addan ke amfani da su a yankin.

Kwamishinan, ya bayyana cewa an gano sansanin ne bayan samun bayanai daga mutanen da aka kama a baya.

Ya yaba da ƙoƙarin haɗin gwiwar jami’an tsaro wajen bibiyar bayanan sirri don daƙile ayyukan ɓata gari a jihar.