’Yan sanda sun dakile harin ’yan bindiga a Kaduna

Maharan sun tare hanyar da nufin sace matafiya, kafin daga bisani ‘yan sanda suka fatattake su.

’Yan sanda sun dakile harin ’yan bindiga a Kaduna

Wasu ‘yan sanda a bakin aiki

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta tabbatar da dakile wani hari da ‘yan bindiga suka kai kan babbar hanyar Buruku zuwa Kaduna.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan ne, ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Kaduna.

A cewarsa ’yan fashin dajin sun tare hanyar da nufin sace matafiya.

“A ranar 21 ga watan Maris, da misalin karfe 1 na rana, jami’an ’yan sandan yankin Buruku sun yi nasarar dakile yunkurin sace mutane a kan babbar hanyar Buruku zuwa Kaduna.

“Rundunar ’yan sanda da hadin gwiwar ’yan banga sun fatattaki maharan zuwa daji.

“Bayan artabun da aka yi da su, wasu daga cikinsu sun samu munanan raunuka yayin arangamar,” in ji shi.

Hassan, ya ce Kwamishinan ’yan sandan jihar, Mista Audu Ali, ya yaba wa namijin kwazon da rundunarsa ta yi na dakile harin.

Ya kuma bukaci jama’ar jihar da kasance masu sanya ido tare da kai rahoton duk wani abu da ba su yarda da shi ba ga jami’an rundunar mafi kusa da su.

Kotu ta yanke wa mutum 5 hukuncin rataya a Kano

NAJERIYA A YAU: Hanyoyin Noma Ba Tare Da Kashe Kuɗi Da Yawa Ba

HOTUNA: Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 4, shanu 15 da awaki 20 a Neja

Mai gari ya tsere bayan mazauna sun cinna wa gidansa wuta a Kano