’Yan sanda sun damke wadanda suke zargi da aikata laifuffuka a Kano

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta baje kolin wasu da take zargi da aikata fashi da makami da kwace motoci da fadawa gidajen mutane da sauransu. Kakakin Rundunar ASP Magaji Musa Majiya ne ya gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai, inda ya ce jami’ansu ne suka damke mutanen a lokuta daban-daban a maboyarsu.Daga […]

’Yan sanda sun damke wadanda suke zargi da aikata laifuffuka a Kano
’Yan sanda sun damke wadanda suke zargi da aikata laifuffuka a Kano

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta baje kolin wasu da take zargi da aikata fashi da makami da kwace motoci da fadawa gidajen mutane da sauransu. Kakakin Rundunar ASP Magaji Musa Majiya ne ya gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai, inda ya ce jami’ansu ne suka damke mutanen a lokuta daban-daban a maboyarsu.
Daga cikin mutanen akwai Hassan Ali mai shekara 58 da Adamu Hashimu mai shekara 50 da ake zargin sun kware wajen kwace motoci daga hannun jama’a. Ya ce su biyun sukan yi amfani da wani sinadari mai bugarwa daga nan sai su yar da mai motar su gudu da ita.
Hassan Ali wanda ya ce shi dan Sabon Birni ne a Jihar Sakkwato da yake da ’ya’ya 23 da mata uku, ya ce a da “Ina sayar da wake da shanu kuma ina noma, daga baya Ubangiji Ya kaddare ni da shiga sata kuma ban wuce shekara biyu da shiga ba.” Ya ce a Minna ta Jihar Neja yana fuskantar irin wannan tuhuma har an kai maganar kotu, sai ’yan sanda daga Kano suka je Minna suka kamo shi, saboda ana nemansa a dalilin kwace wata tifa da ya yi, wacce aka taho da ita daga Lome ta kasar Togo, bayan ya ba mai ita maganin kawar da hankali mutumin ya rasu.
Ya ce ya yi irin haka kamar sau biyar ne kuma idan sun sayar da motar da suka kwace yana sayen abinci ne ga iyalansa, wadanda ya ce ba su san yana sata ba. Ya ce daga cikin abokan satarsa har da wani Yahaya dan Birnin Kebbi da Mustafa dan Hadeja.
Shi kuwa Hashimu ya ce yana sana’ar ga-ruwa a unguwar Sabon Gari daga nan sai ya koma yaron mota kuma ya zama direba inda ya koma Rimin Kebe da zama. Ya ce daga nan ya shiga sana’ar hada barayin motocin da masu saye. Ya ce shi ne ya hada Hassan da wani mai suna Sunusi, yana sayen motocin da ya sato.
Kakakin ’yan sandan ya ce suna ci gaba da binciken wadanda ake zargi kuma za su mika su ga kotu da zarar sun kammala bincikensu. Ya bukaci jama’a su rika ba jami’an tsaro bayani da zarar sun ga batagari a unguwanninsu.