’Yan sanda sun far wa wakilan Aminiya da BBC a kotun zaben gwamnan Kano

Sun fasa fuskar wayar wakilin Daily Trust, tare da yunkurin kwace ta wakilin BBC

’Yan sanda sun far wa wakilan Aminiya da BBC a kotun zaben gwamnan Kano

’Yan sanda sun far wa ’yan jaridar kafofin yada labaran Daily Trust da takwaransa na BBC a yayin da suka ke daukar rahoto a kotun sauraron kararrkin zaben gwamnan Kano, wadda a yau za ta yanke hukunci.

Zahraddeen Lawa na BBC da Salim Umar Ibrahim na Daily Trust sun fuskanci hakan ne daga ’yan sandan da aka girke a wurin da kotun za ta yi zaman.

Da farko ’yan sandan sun umarci ’yan jaridar su yi nesa da baya da kimanin mita 10.

Ana cikin haka ne waus daga cikin jamia’n tsaro suka fara cin mutuncin ’yan jaridar, wai suna daukar hoto.

’Yan sandan sun yi cakumi wakilin BBC suna kokarin kwace wayasa daga aljihunsa,a yayin da wasu suka nemi kwace wayar takwaransa na Daily Trust, inda a garin haka suka fasa fuskar wayar.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan