’Yan sanda na farauta masu yunkuri hana rantsar da Tinubu

Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, ne ya sanar da haka a safiyar Litinin.

’Yan sanda na farauta masu yunkuri hana rantsar da Tinubu

Hukumomin tsaro a Najeriya sun kaddamar fa farautar ’yan siyasar da ake zargi da yunkurin kawo cikas ga rantsar da shugaban kasa mai jiran gado, Bola Tinubu da mataikainsa, Kashim Shettima, a ranar 29 ga watan Mayu.

Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Usman Baba Alkali, ya sanar a safiyar Litinin a Hedikwatar rundunar cewa suna gudanar da aikin ne da hadin gwiwar hukumomin leken asiri da sauran hukumomin tsaro.

Ya ce yin hakan na muhimmanci domin dakile masu neman tayar da zaune tsaye a Najeriya.

“Mun lura bayan zaben shugaban kasa, wasu ’yan si’asa da sakamakon bai yi musu dadi na ta barazana da nufin tayar da fitinia domin hana rantsar da sabon shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu.

“’Yan sanda da sauran hukumomin tsaro na aiki tare wajen lura da motsin wadannan ’yan siyasa da sauransu da suke rudin kansu da yunkurin barazana ga tsaron kasa.”

Don haka ya ce hukumomin tsaro ba za su lamunci duk wani furuci da ke iya tayar da fitina daga kowane irin mutum ba, komai matsayinsa.

“Rundunar ’yan sanda na gargadin duk ’yan siyasa da yaransu da kuma abokansu masu irin wannan manufa da su shiga hankalinsu a yunkurin da suke na kawo wa bikin ranar 29 ga wata cikas.”