’Yan sanda sun fara sintiri ta sama a Jihar Nasarawa don magance rikici

Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya mai kula da al’amuran sararin samaniya A.I.G Ileseni Awuda ya ba al’ummar Jihar Nasarawa tabbacin ba da kariya ga rayuka da dukiyarsu oyinsu. A.I.G Awuda ya bayyana haka ne kafin ya soma kewaya sararin samaniyar jihar domin tabbatar da tsaro a makon jiya sakamakon matsalar rashin tsaro da […]

’Yan sanda sun fara sintiri ta sama a Jihar Nasarawa don magance rikici
’Yan sanda sun fara sintiri ta sama a Jihar Nasarawa don magance rikici

Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya mai kula da al’amuran sararin samaniya A.I.G Ileseni Awuda ya ba al’ummar Jihar Nasarawa tabbacin ba da kariya ga rayuka da dukiyarsu oyinsu. A.I.G Awuda ya bayyana haka ne kafin ya soma kewaya sararin samaniyar jihar domin tabbatar da tsaro a makon jiya sakamakon matsalar rashin tsaro da jihar ta tsinci kanta a ciki musamman a kudancin jihar.
Ya ce rundunar ta dauki matakin yin sintiri a sararin samaniyar jihar ne musamman a garurruwa da kauyuka da kan iyakan jihar da lamarin ya fi muni ta amfani da jirgin sama mai saukar ungulu a kowane bangaren jihar.
Ya ce “Wannan kewayewa da za mu yi a sararin samaniyar jihar nan za mu yi ne domin samar da zaman lafiya. Idan kuka duba kusa da ku za ka ga yawancin manyan wuraren ’yan sanda ne aka kakkafa. Haka ma idan kuka je kauyuka za ku ga ’yan sanda ne aka kakkafa a wuraren domin daukar matakan da za su tabbatar da zaman lafiya.”
A.I.G Awuda ya bayyana cewarashin tsaro a jihar ya samo asali ne daga bakin iyakar jihar, inda a cewarsa yanzu rundunar ta dauki matakai masu muhimmanci domin magance lamarin. Daga nan sai ya yi kira ga kabilun jihar su tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da jituwa a tsakaninsu, don ba gwamnati damar samar musu da ribar dimokuradiyya.
Ya ce a nata bangare rundunar ’yan sandan ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na kawo karshen tashin-tashina a jihar da kansar nan baki daya ba, kuma za ta tabbatar an hukunta duk wanda aka kama yana tada zaune-tsaye.