’Yan sanda sun fatattaki bata-gari daga Kasuwar Lemo ta Maraba
An yaba wa ’yan sandan yankin Mararraba a karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa dangane da magance ta’asar da wadansu batagari ke tafkawa a Kasuwar Lemo da aka fi sani da ‘Orange Market’ da ke Mararraba. Wadansu ’yan kasuwa da suka bukaci a sakaye sunayensu ne suka shaida wa wakilinmu haka lokacin da suke tattaunawa […]
An yaba wa ’yan sandan yankin Mararraba a karamar Hukumar Karu a Jihar Nasarawa dangane da magance ta’asar da wadansu batagari ke tafkawa a Kasuwar Lemo da aka fi sani da ‘Orange Market’ da ke Mararraba. Wadansu ’yan kasuwa da suka bukaci a sakaye sunayensu ne suka shaida wa wakilinmu haka lokacin da suke tattaunawa a kasuwar, inda suka ce a kwanakin baya batagari sun yi wa kasuwar kawanya, inda manyan masu aikata miyagun laifuffuka da suka hada da yin garkuwa da mutane da fashi a shaguna da gidaje da sha tare da sayar da wiwi, suka baje kolinsu. Sun kuma ce an rika shigo da haramatattun kayayyaki cikin kasuwar ana kasawa a fili, kamar yadda ake kasa tumatur ba tare da tsoro ba.
Yanzu kuwa a cewarsu, wadannan ayyukan ta’asa da suka zame musu alakakai suke jawo musu zaman dar-dar yanzu sun zama tarihi, sakamakon kai farmakin da ’yan sandan yankin a karkashin jagorancin DPO Abdullahi Liman suka yi ga wadanda ake zargin. Sun kuma ce a yanzu ’yan sandan suna gudanar da sintiri a kasuwar da yankin baki daya ba dare ba rana, inda suka kame tare da hukunta wadannan batagari.
Sun kara da cewa a halin yanzu ’yan kasuwar suna gudanar da harkokinsu cikin lumana da kwanyiyar hankali sakamakon isasshen tsaro da ’yan sandan suka tabbatar a kasuwar da yankin baki daya, don haka suka yi kira ga ’yan sandan cewa, “Su dore da wannan namijin kokari. da suke yi”
Da Aminiya ta tuntubi Shugaban ’Yan sandan a ofishin rundunar na yankin, DPO Abdullahi Liman, ya ce jim kadan da samun labarin ayyukan batagarin bai yi wata-wata ba ya umarci jami’ansa tare da hadin gwiwar jami’an tsaron sirri da ’yan banga suka kai samame na musamman a kasuwar da kewayenta. Ya ce sun gano tare da kama miyagun mutane kuma sun ladabtar da su tare da hukunta su.
Ya ce a halin yanzu binciken da rundunar ta yi ya nuna cewa ana samun gagarumar nasara a bangaren tsaro a kasuwar da yankin baki daya sakamakon sintiri da jami’ansa tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro suke gudanarwa a yankin a kai-a kai a kullum. Sai ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Nasarawa su tallafa musu da isassun kayayyakin aiki, musamman motocin sintiri da gina musu ofishinsu na dindindin da inganta jin dadin jami’ansu da sauransu don ba su damar ci gaba da gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.