’Yan sanda sun fatattaki ‘yan bindiga a Abuja

Rundunar ta jadadda aniyar samar sa tsaro a fadin Najeriya.

’Yan sanda sun fatattaki ‘yan bindiga a Abuja

Rundunar ’Yan Sandan Birnin Tarayya, sun kai farmaki tare da kashe wasu kasurguman ’yan bindiga a sansaninsu da ke unguwar Mpape, a Abuja.

Wata sanarwa da kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar a Abuja, ya ce an kai samamen ne a ranar 9 ga watan Fabrairu bayan samun bayanan sirri.

Ya ce, sun yi nasarar kashe wasu kasurguman mahara a maboyar.

Ya ce sun hallaka kasurgumin dan bindigar da ya addabi yankunan Mpape, Bwari a Abuja, Kagarko a Kaduna, Masaka da kuma kauyen Nukun a Jihar Nasarawa.

A cewarsa, maharan sun jima suna satar mutane tare da karbar kudin fansa.

Kazalika, ya ce sun samu nasarar kai farmakin ne a maboyarsu da ke wani tsauni a Mpape tare da kwato makamai.

Adejobi, ya ce sun kwato makamai da suka hada da wayoyin hannu, layin waya, laya da kuma kwayoyi.

Ragowar sun hada da alburusai, adda, wukake da sauran muggan makamai.

Adejobi, ya ce rundunar ’yan sandan Najeriya za ta ci gaba da jajircewa wajen yaki da miyagun laifuka da kuma tabbatar da tsaro a fadin kasar nan.

Ya ce, rundunar za ta ci gaba da daukar matakan da suka dace don kama masu laifi, tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe

Iran da Amurka sun daidaita tattaunawar sulhu a Switzerland