’Yan sanda sun gabatar da Hakimi a cikin ’yan fashi

A makon jiya ne rundunar ‘yansandan jihar Zamfara ta kama wani uban kasa na riko na garin Keta da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, mai suna Mainasara ‘Yandoto tare da wadansu mutane tana zarginsa da laifin hada baki da wadansu mutane suka yi fashin kudi har naira dubu dari da hamsin tare da […]

’Yan sanda sun gabatar da Hakimi a cikin ’yan fashi

Hakimi (na biyu daga dama sanye da shudiyar riga) tare da sauran ‘yan fashin da ake zargiA makon jiya ne rundunar ‘yansandan jihar Zamfara ta kama wani uban kasa na riko na garin Keta da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara, mai suna Mainasara ‘Yandoto tare da wadansu mutane tana zarginsa da laifin hada baki da wadansu mutane suka yi fashin kudi har naira dubu dari da hamsin tare da wadansu kayayyaki.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Zamfara, ASP Lawal Abdullahi ne ya bayyana haka ga manema labarai a ofishinsa da ke Gusau.
Ana zargin cewa hakimin ya hada kai ne da wadansu mutane suka shiga gidajen Musa Tukur da Alhaji Haruna Amadu da Mu’azu Atta Alaramma da kuma Hamza Alhaji Wakili, inda suka sace musu kudi har dubu dari da hamsin tare da wadansu kayayyaki.
ASP Lawal ya kara da cewa, wadanda ake zargin sun kuma kama  matar wani mai suna Muhammad Lawali suka yi mata fyade bayan sun tura shi mijin nata cikin daji suka boye shi. Ya ce rundunarsu ta samu nasarar gano Naira dubu13 daga cikin kudin da suka sato, kuma shi uban kasar Malam Mainasara ya amfana da Naira dubu ashirin daga cikin kudin.
A zantawar da wakilinmu ya yi da daya daga cikin wadanda ake zargin, ya bayyana cewa su ba su yi wa kowa fashi ba kuma bai yarda da zargin da ake yi musu ba.
 Wakilinmu ya ziyarci garin Tsafe don jin ta bakin mazauna garin kan halin uban kasar, inda wata majiya ta bayyana wa wakilin namu cewa shi dai Malam Mainasara dan sarauta ne kuma Mai martaba sarkin Tsafe shi ne ya tura shi garin Keta don ya rike masarautar a sakamakon rasuwar sarkin garin, kuma saboda takaddamar da take tattare da gidan sarautar ce ta sanya har yanzu ba a nada wanda zai hau kan wannan kujerar ba, har ga shi an kwashe sama da shera guda da rasuwar tsohon sarkin.
Wata majiya kuma ta bayyana wa wakilinmu cewa kafin Mai martaba ya tura Mainasara garin Keta kowa ya sanshi kuma ya san halinsa ,don haka jama’a da dama ba su yi mamaki ba lokacin da aka ce shi ne aka tura garin na keta, don kowa ya san tsohon ma’aikaci ne na karamar Hukumar Tsafe da ya yi aiki a fannin lafiya daga baya ya bari.
A  zantawar da Aminiya ta yi da wani mai suna Abdullahi mazaunin garin  na Tsafe, ya bayyana wa wakilinmu cewa, kowa ya san yadda shi Mainasara yake. Na farko dai ba ya zama sosai a garin na Keta kuma daga bayan nan yana yawan kebewa da wadansu wadanda kowa ya san cewa suna da matsala matuka. Sai dai wadansu sun ce su a tsammaninsu huldar da ya kulla da wadannan mutanen ba ta rasa nasaba da ababen da ake zarginsu da su, domin kowa ya san wadannan mutanen ‘yan rigima ne, ba su tsoron shari’a, ko da wa za ta kaya.
Shi ma Malam Aliyu wani mazaunin garin Keta ne, ya bayyana wa wakilinmu cewa su kam sun ji dadi da Allah yake tona asirin wadansu mutane da babu wanda zai yarda suna aikata mugun aiki. Ya kara da cewa su ba za su taba yarda Mainasara ya sake dawowa garin su ya zauna ba, sai dai shi Mai martaba Sarkin Tsafe ya dauko wani daga Tsafe ko danjibga Ko kuma nan garin na Keta, tun da gidajen sarautar da ake da su guda hudu ne, daga ko’ina ana iya dauko wani a sanya musu, amma ba wanda yake hada kai da barayi ana cutarsu ba.
Shi ma Malam Musa wani mazaunin Keta ne, ya bayana cewa, tun da aka kawo Mainasara garin Keta ba su sonsa kuma ba su jin dadinsa. Kuma a cewarsa, wadansu suna zargin Mainasara da hada baki da wadansu ana cutarsu, kamar ‘yansandan garin na Keta. Domin haka ya ce su kam babu abin da za su ce sai dai Allah ne kawai zai yi hukunci tsakaninsu da wadanda suke cutar da su, kowa ya san yadda Mainasara yake kafin tafiyarsa Keta, amma yanzu kowa zai iya sanya alamar tambaya a kansa.
Wakilinmu ya sake komawa wajen jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yasandan jihar Zamfara domin ya ba Aminiya dama ta ji ta bakin Mainasara ‘Yandoto wanda a halin yanzu yake tsare a wurinsu, amma abin ya ci tura, don ASP Lawal Abdullahi ya bayyana wa wakiinmu cewa an garzaya da wadanda ake zargin zuwa kotu don yi musu shari’a.
 Aminiya ta kuma nemi jin ta bakin Mai martaba Sarkin Tsafe Alhaji Habib Aliyu ko wani daga masarautar ta Tsafe amma abin ya ci tura.