’Yan sanda sun gabatar da yarinyar da ta yi jigida da bam

A Larabar da ta gabata ce Hukumar ’yan sanda a Kano suka gabatar wa manema labarai wata yarinya mai suna Zahra’u Babban Gida, wacce suka ce sun kama ta tana daure da bama-bamai, a Kantin Kwari kwanakin baya.Yarinyar mai matsakaicin shekaru, ta yi ikirarin cewa an sace ta ne daga Jihar Bauchi kuma tun daga […]

’Yan sanda sun gabatar da yarinyar da ta yi jigida da bam

Zahra’u, yarinyar da aka kama da bamA Larabar da ta gabata ce Hukumar ’yan sanda a Kano suka gabatar wa manema labarai wata yarinya mai suna Zahra’u Babban Gida, wacce suka ce sun kama ta tana daure da bama-bamai, a Kantin Kwari kwanakin baya.
Yarinyar mai matsakaicin shekaru, ta yi ikirarin cewa an sace ta ne daga Jihar Bauchi kuma tun daga lokacin ba ta cikin hayyacinta har sai a ranar da aka gabatar da ita ga manema labaran.
Tun da farko dai, ’yan sandan sun ce an kama Zahra’u ne a daura da kasuwar Kantin Kwari, daidai wurin da bama-bamai biyu suka tarwatse makonni biyu da suka gabata, wadanda aka yi zargin wasu mata ne biyu suka tarwatsa su; al’amarin da ya haddasa mutuwar wasu mutane da dama.
Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Kano, Alhaji Tashid Aderile Shinaba ya ce jami’ansa sun kama yarinyar ne a sakamakon zarginta da suka yi, musamman yadda ta rika kai-komo a harabar kasuwar. Ya ce bayan sun kama ta ne aka tafi da ita hedikwatar ’yan sanda, inda su ma jami’an SSS suka hadu da su domin ci gaba da bincike.