’Yan sanda sun gano katinan zaben da aka sace a Legas
Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta gano tare da kwato katunan zabe na dindindin kimanin dubu daya da dari 700, wadanda ake zargin an sace su ne daga ofishin hukumar zabe ta INEC a karamar Hukumar Ajeromi Ifelodun da ke jihar Legas.’Yan sandan sun gano katunan ne a cikin daji a kan iyakar Najeriya da […]
Rundunar ’yan sandan jihar Legas ta gano tare da kwato katunan zabe na dindindin kimanin dubu daya da dari 700, wadanda ake zargin an sace su ne daga ofishin hukumar zabe ta INEC a karamar Hukumar Ajeromi Ifelodun da ke jihar Legas.
’Yan sandan sun gano katunan ne a cikin daji a kan iyakar Najeriya da kasar Binin daidai yankin garin Badagiri.
Aminiya ta gano cewa ’yan sandan sun samu nasarar gano katunan ne bayan da rundunar ta samu bayanan sirri karkashin jagorancin kwamandan shiyya ta ‘K’ da mataimakin kwamishinan ’yan sanda yayin da suke binciken dajin.
Wani jami’I, wanda ya yi ikirarin kasancewa daya daga cikin wadanda suka binciki dajin, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce sun dauki tsawon sa’o’i da dama kafin su gano inda aka boye katunan zaben a wata bakar jaka.
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar Kenneth Nwosu, ya ce binciken farko ya nuna cewa ta yiwu an sato katunan ne daga ofishin hukumar zabe ta INEC.
Ya gargadi ’yan siyasa da suke da burin satar kayan zabe su guji yin haka, inda ya kara da cewa duk wanda aka kama zai dandana kudarsa.
Ya bayyana cewa ana ci gaba da bincike don gano wadanda suka sace, tare da boye katunan, ta yadda za a gurfanar da su a gaban kotu.