’Yan sanda sun gano shanun sata 108 da tumaki 18 a Abuja

Rundunar ’yan sanda ta yankin birnin tarayya Abuja ta gano shanun sata 108, da tumaki 18, da kuma bindigogi bayan sun yi kutse a wata rugar makiyaya a kauyen Chitimu da ke kusa da garin Zuba a yankin Abuja. Kwamishinan ’yansanda na yankin Mista Wilson Inalegwu wanda ya bayyana hakan a hedikwatar rundunar a ranar Litinin […]

’Yan sanda sun gano shanun sata 108 da tumaki 18 a Abuja
’Yan sanda sun gano shanun sata 108 da tumaki 18 a Abuja

Rundunar ’yan sanda ta yankin birnin tarayya Abuja ta gano shanun sata 108, da tumaki 18, da kuma bindigogi bayan sun yi kutse a wata rugar makiyaya a kauyen Chitimu da ke kusa da garin Zuba a yankin Abuja.
 Kwamishinan ’yansanda na yankin Mista Wilson Inalegwu wanda ya bayyana hakan a hedikwatar rundunar a ranar Litinin da ta gabata a yayin baje kolin wasu da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban da rundunar ta kama a cikin mako biyu da suka gabata, ya shaidawa manema labarai cewa rundunarsa ta kuma kama mutum shida da ake zargi da hanu a satar dabbobin wanda yawancinsu an sato su ne daga kauyen Farakwai da ke Jihar Kaduna. Ya ce wadanda aka kaman sun hada da Musa Magaji, da Sulaiman Abubakar, da Abubakar Sule, da Garba Musa, da kuma Yahaya Sulaiman.
Haka nan Kwamishinan na ’yan sanda ya kuma nuna nau’ukan bindigogi daban-daban da suka hada da bindigar adaka guda biyu, da karamar bindiga ta hannu kirar gida, da dobul barel guda daya, da kuma wata bindiga kirar kamfani.
A zantawarsu da Aminiya, wani daga cikin wadanda ake zargin mai suna Abubakar Sule, ya amsa cewa ya sato shanu hamsin daga  Jihar Kaduna a farkon waannan shekara, sai dai ya ce ragowar hamsin din na wasu mutum biyu ne da kowannensu ya mika masa dabbobinsa don yi masa kiwo.
A bayaninsa ga Aminiya wani wanda ake zargin mai suna Musa Magaji wanda ya ce shi mazaunin garin Ayingba ne da ke Jihar Kogi, ya ce ya baro gida a ranar Lahadin da ta gabata bayan daya daga cikin wadanda ake zargin ya yi masa waya inda a cewarsa ya sanar da shi cewa wani manomi ya datse hannun daya daga cikin yaransa da ke yi masa kiwo bayan wani sabani.
Ya ce wanda ake zargin wanda shi ke jagorantar kula da dabbobin nasa ya sanar da shi cewa lamarin na gaban ofishin ’yan sanda na Zuba, amma yana isa wajen sai aka kama shi aka kuma mikashi ga rundunar ’yansanda ta Abuja.
Ya ce ya gane dabbobinsa a cikin wadanda aka kama kuma ya ce ba sa cikin shanun da aka kama tun da farko ya ce ya sato.
Shi ko Garba Musa wani daga cikin wadanda ake zargin cewa ya yi, an kama shi ne a lokacin da ya je ofishin na ’yansanda don neman dabbobinsa bayan ya samu labarin an kama su a daidai lokacin da yake jayayya da daya daga cikin wadanda ake zargin kan mallakan wasu dabobi.
Kwamishinan na ’yansanda ya ce duk wadanda ake zargin za a gurfanar da su a gaban kotu bayan sun kamalla bincike.