’Yan sanda sun gano shanun sata 112 tare da kama varayi uku a dajin Kaduna
Wani sashi na musamman da ofishin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ya kafa don yaqi da satar shanu, ya gano ximbin shanun sata 112 da tumaki fiye da 30 tare da kama waxanda ake zargi varayin shanu ne a wani daji da ke iyakar Jihar Kaduna da Nasarawa. Bayanai sun ce ana kyautata zaton […]
Wani sashi na musamman da ofishin Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ya kafa don yaqi da satar shanu, ya gano ximbin shanun sata 112 da tumaki fiye da 30 tare da kama waxanda ake zargi varayin shanu ne a wani daji da ke iyakar Jihar Kaduna da Nasarawa. Bayanai sun ce ana kyautata zaton an sato shanun da tumakin ne daga jihohin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.