’Yan sanda sun gano wata mota da aka sace shekaru biyar da suka gabata
Bincike ya nuna gano cewa an kai motar Jamhuriyar Nijar a shekarar 2023, sannan aka dawo da ita Najeriya a watan Oktoban 2025.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta gano wata mota ƙirar Toyota Highlander da aka sace a Jihar Ribas kimanin shekaru biyar da suka gabata, bayan an gano ta yayin ƙoƙarin sake yi mata rajista a jihar.
A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya fitar ya bayyana cewa an gano motar mai lambar rajista FH823PHC a ranar 8 ga Yunin 2026.
- APC ta lashe zaɓen cike gurbin da aka gudanar a Kano
- Majalisar Ɗinkin Duniya ta musanta zargin yi wa Kiristoci kisan ƙare dangi a Najeriya
Ya ce an gano motar ce yayin wani aikin tantance bayanan ababen hawa da jami’an Sashen Leken Asiri (SID) suka gudanar tare da haɗin gwiwar Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) a ofishin rajistar ababen hawa na Hukumar Tara Haraji ta Jihar Gombe.
Bincike na farko ya nuna cewa motar mallakin Misis Cecilia A. Duru ce daga Rumuodumaya da ke Fatakwal, kuma an bayar da rahoton sace ta tun ranar 17 ga Satumbar 2021.
A cewar rundunar, bincike ya kuma gano cewa an kai motar Jamhuriyar Nijar a shekarar 2023, sannan aka dawo da ita Najeriya ta ƙaramar hukumar Illela a Jihar Sakkwato a watan Oktoban 2025.
Daga bisani, an sayar da motar a Jihar Kaduna kafin a kawo ta Gombe domin sake yi mata rajista, inda aka gano sahihancin bayananta ta hanyar binciken tsarin rajistar ababen hawa.
Rundunar ’yan sandan ta ce tana ci gaba da bincike domin gano tare da cafke waɗanda ke da hannu a satar motar da safararta zuwa ƙasashen waje da kuma sayar da ita.
DSP Buhari Abdullahi ya shawarci masu sayen motocin hannu da su tabbatar da sahihancin takardun mallaka kafin kammala ciniki, tare da jaddada ƙudirin rundunar na yaƙi da satar ababen hawa da sauran laifuffuka.
