’Yan sanda sun gano wuraren kera bindigogi a Jihar Kaduna
A shekaranjiya Laraban ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ta ce ta gano masana’antun kera bindigogi a wasu garuruwan Kuduncin jihar.A cewar rundunar, wadanda ake zargi da mallakar masana’antun suna kera makaman ne su raba wa masu aikata laifuffuka a yankin.Da yake gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Shehu […]
A shekaranjiya Laraban ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna ta ce ta gano masana’antun kera bindigogi a wasu garuruwan Kuduncin jihar.
A cewar rundunar, wadanda ake zargi da mallakar masana’antun suna kera makaman ne su raba wa masu aikata laifuffuka a yankin.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin ga manema labarai, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Shehu Usman ya ce ’yan sandan da ke aiki a yankin Kafanchan ne suka yi nasarar kama mutanen a garuruwan kaura da Zangon Kataf.
“Wadanda ake zargin an same su ne a masana’antunsu da ke yankin Kudancin Kaduna inda suke kera bindigogi suna bai wa batagari domin su rika addabar jama’ar yankin.
Wadanda muka kama ga sunayensu kamar haka Isah Yahaya da Zamari Peter da Baye Tswan dukkansu a garin Mabushi da ke karamar Hukumar kaura sai kuma Felid Paul daga Samaru a karamar Hukumar Zangon Kataf.”
Ya ce “A lokacin wannan samame da muka kai, an samu bindigogin da aka kera guda 37 da kuma kananan bindigogin hannu 11 sai wasu samfurin bindigogi 34.”
Kwamishinan ya kuma bayyana cewa an gano bindigogin toka guda biyu da harsasai da sauran wasu abubuwan kera miyagun bindigogi.
Da Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i da yake zantawa da manema labarai a kan wannan nasara da randunar ta samu ta bakin kakakinsa Samuel Aruwan a Hedkwatar ’Yan sandan Jihar, ya ce duk wanda aka kama da makami dole ne a hukunta shi. Ya ce gwamnatin jihar ta sha alwashin kawar da batagari daga cikin al’ummar jihar.