’Yan sanda sun gargadi masu tashe kan tayar da hankali a Kano

Rundunar ta ce za ta sa kafar wando daya da duk wanda aka kama na shirin tada zaune-tsaye.

’Yan sanda sun gargadi masu tashe kan tayar da hankali a Kano

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, ta ce ta dauki kwararan matakan tsaro domin tunkarar masu shirin tada zaune-tsaye yayin bikin al’adar tashe ta bana a jihar.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel, ya ce an yi nazari sosai kan yadda ake aikata laifuka a jihar, kuma an gano cewa wasu matasa na shiriin fakewa da al’adar “Tashe” don haifar da rashin tsaro a jihar.”

Gumel, ya ce: “Watanni uku da suka gabata mun gano wasu matasa da suke shirin yin fadan daba, domin su farmaki mutane, su kwace musu dukiya da sunan tashe.”

Ya ce saboda haka ne rundunar ‘yan sandan jihar ta dauki kwararan matakan tsaro domin magance kalubalen da iya hana lafiya a sassan jihar.

Gumel, ya kara da cewa, zuwa yanzu sun umarci DPI na kowane ofishin ’yan sanda, da su tashi tsaye domin dakile duk wani yunkuri na tayar da hankalin mutane yayin tashe da ke tafe.

Kwamishinan, ya tabbatar da cewa, sashen leken asiri na rundunar ya kara zage damtse don tunkarar barazanar tsaro da ke shirin kunno kai da sunan tashe.

Ya kuma nemi hadin kan al’umma da su taimaka wa jami’ansu wajen ba su bayanai game da duk wani abu da zai iya shafar tsaro a lokacin tashe da ma bayan Ramadan.

Rundunar ta kuma gayyaci wasu shugabannin al’umma, da suka hada da malaman addini da shugabannin matasa domin tattaunawa kan yadda za a shawo kan matsalar tsaro musamman a tsakanin matasan da ke amfani da tashe wajen aikata laifuka maimakon bunkasa al’adar tashen.

Don namen mulki ’yan siyasa ke sukan Tinubu —Gwamnan Kaduna

Alakarmu da El-Rufai na nan babu matsala —Uba Sani

Yau Majalisar za ta ci gaba da aiki kan Dokar Haraji

Kotu ta tsige Ohinoyi na Ƙasar Ebira