’Yan sanda sun gurfanar da wani mai haramtaccen asibitin ido a Uyo

Wani mai haramtaccen asibitin ido mai suna Sahal Specialist Eye Clinic da ke Uyo,  Dokta Hussaini Yusuf Arugaya ya musanta laifinsa, yayin da rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom ta kama shi ta kuma gurfanar da shi gaban kotun majistare a Uyo. Ana zargin Dokta Hussaini tare da tuhumarsa da aikata laifuka uku da suka […]

’Yan sanda sun gurfanar da wani mai haramtaccen asibitin ido a Uyo

Wani mai haramtaccen asibitin ido mai suna Sahal Specialist Eye Clinic da ke Uyo,  Dokta Hussaini Yusuf Arugaya ya musanta laifinsa, yayin da rundunar ’yan sandan Jihar Akwa Ibom ta kama shi ta kuma gurfanar da shi gaban kotun majistare a Uyo.
Ana zargin Dokta Hussaini tare da tuhumarsa da aikata laifuka uku da suka hada da bayyana kansa a matsayin kwararren likitan ido, sannan kuma sai yi wa wani dattijo mai suna Ndarake Akpe tiyata a idonsa na dama, sai kuma amfani da kalmar dokta wato likita, wanda hakan ke nuna kamar doka ta amince masa ya yi aikin likita.
Aminiya ta halarci zaman kotun da aka bayyana shi a matsayin likitan jabu da ba shi da rajistar yin aiki, sannan kuma ya bude asibitin yana gudanar da aiki ba tare da ka’ida ko izini daga  hukuma ba, wanda yin hakan ya saba wa sashe na 17 [1] [a] na dokar bayar da izinin aiki na kungiyar masu aikin likita da kula da hakora ta Nijeriya da sashe na 17 [15] [b] na doka mai suna Cap M8 ta tsarin  kundin mulkin Najeriya 2004. Sannan a ranar 26 ga watan Yulin shekarar 2011 ya yi wa wani mutum tiyata a idonsa na dama a garin Eket.
Bayan da alkalin kotu ya gama karanta wa wanda ake zargi laifinsa, Husaini Arugaya ya ki ya amsa laifinsa da ake zarginsa da aikatawa. Lauyan wanda ake kara, Mista Akanimoh Asukuo ya nemi a ba shi belinsa, kuma alkalin kotun, Mai shari’a Lawrence Udenwa ya amince ya kuma ba da belinsa kan Naira  dubu dari uku.