’Yan sanda sun hana taron Jam’iyyar APC na Sakkwato armashi
A ranar Litinin da ta gabata ne aka yi taron gangami da rantsar da shugabannin Jam’iyYar APC na shiyyar Arewa maso Yamma a Sakkwato, inda ’yan sanda suka jefa wa mahalarta taron borkon tsohuwa.Taron ya gudana ne a filin Kasuwar Baje-Koli da ke Unguwar Mabera Mujaya a garin Sakkwato, inda jami’an tsaro suka hana wa […]
A ranar Litinin da ta gabata ne aka yi taron gangami da rantsar da shugabannin Jam’iyYar APC na shiyyar Arewa maso Yamma a Sakkwato, inda ’yan sanda suka jefa wa mahalarta taron borkon tsohuwa.
Taron ya gudana ne a filin Kasuwar Baje-Koli da ke Unguwar Mabera Mujaya a garin Sakkwato, inda jami’an tsaro suka hana wa taron armashi saboda jefa borkonon tsohuwa har sau uku, daya a gefen dandalin taron a daidai lokacin da Shugaban Jam’iyyar APC ta kasa Cif John Onyegun ke jawabi.
Hayakin borkonon ya turnuke dandalin taron inda ya sanya manyan mutanen da ke saman dandalin zubar da hawaye, kuma ya kawo karshen jawabin shugaban, wanda ya hanzarta kaddamar shugabanin, kuma nan take ya bar dandalin zuwa babbar rumfa.
Borkonon na biyu kuwa an watsa shi ne a wajen filin taron inda iskarsa ta mamaye mahalarta taron suka rika gudu suna barin filin domin tsira da lafiyarsu.
Na uku kuwa an jefa shi ne a gefen filin inda mambobin jam’iyyar suka fice ta hanyar haura kataga domin tsira da lafiyarsu.
Barkonon tsohuwar da aka rika watsawa a filin taron ba a san dalilin sa ba, sai dai Gwamnan Jihar Kano ya yi jawabi kafin fesa borkonon inda ya ce, za su nuna wa Shugaban kasa Goodluck Jonathan hanyar fita daga fadar Shugaban kasa a badi, domin mutanen kasar nan sun gaji da gurbatacciyar gwamnati suna bukatar canji.
Ya ci ga da cewa, “Za mu karbi shugabanci daga hannun PDP, duk wani mai son ci gaba a kasar nan ba da jimawa ba zai shiga wannan jam’iyya ta APC. Shekara 16 na jagorancin PDP ya kare da haka nake kiran gwamnonin Jigawa da Neja su zo mu yi wannan tafiya tare domin manufarmu daya gidajenmu daya.”
Gwamna Kwankwaso ya yi kira ga gwamnonin yankin da suka rage, su shiga APC domin ceto yankin da kasa baki daya daga kara shiga mayuwacin hali. “kasar nan tana cikin matsala, shiga APC ne kawai zai iya fito da wannan kasar a samu dorewar zaman lafiya da hadin kan da aka san kasar nan da shi,” inji shi.
Gwamna Kwankwaso ya ce “A yanzu kusan mutum miliyan hudu ne ke gudun hijira a cikin kasa da wajenta, sun bar gidajensu amma ba wani kwararan matakki da aka dauka. Ina ’yan matan Chibok har an fara mantawa da su, wannan kasar na bukatar canji.”
Gwamnonin jihohin Sakkwato da Zamfara da Imo da Edo a jawabansu mabanbanta sun yi kira ga ’yan Najeriya su fito domin a kawar da wannan gwamnati da ta sanya kasa cikin matsala da rashin aikin yi da rashin tsaro a cikin shekara 16 da ta yi tana mulki.
Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na Arewa maso Yamma Alhaji Inuwa Abdulkadir ya gode wa jagororin jam’iyyar da suka aza musu wannan aiki, tare da tabbatar musu cewa ba za su ba su kunya ba har sai sun ga an samu nasara.
Ya ce duk da wasu sun so su ga wannan taro bai gudana ba, amma Allah Ya nufa an yi lafiya an kare lafiya, kuma insha Allah, APC za ta samu nasara a zaben 2015.