Tsaro: An haramta aikin ’yan banga a Kano
Rundunar ’yan sandan Kano ta haramta wa ’yan banga da mafarauta gudanar da ayyukan samar da tsaro a jihar
Rundunar ’yan sandan Kano ta haramta wa ’yan banga da mafarauta gudanar da ayyukan samar da tsaro a jihar.
Kakakin rundunar, Abdullahi Haruna Kiyawa ya sanar a ranar Alhamis cewa ba a yarda ’yan banga ko mafarauta su yi aikin samar da tsaro a ko’ina a jihar ba.
“Domin kawar da shakku, an dakatar da ’yan banga da mafarauta da dangoginsu daga shiga cikin aikin samar da tsaro,” in ji rundunar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta fito ne a yayin da Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano take shirin yanke hukunci kan shari’ar dambarwar masarautun jihar.
- An kashe matashi kan batanci ga Annabi (SAW) a Bauchi
- NAJERIYA A YAU: Yadda Za Ku Fahimci Hukuncin Shari’ar Masarautun Kano Dalla-Dalla
Rundunar ta ce ya zama wajibi ta ba wa jama’ar jihar cikakken tsaro daga masu neman tayar da fitina, lura da yadda shari’ar ke sa mutane zullumi.
“A yayin da ake jan hankalin mutane da masu neman tayar da fitina su shiga taitayinsu, ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro za su ci gaba aiwatar da dokar haramta zanga-zanga da dangoginsa a fadin jihar.
“Za a kama duk wanda ya taka dokar tare da gurfanar da shi domin ya girbi abin da ya shuka,” in ji sanarwar rundunar.
Kiyawa ya kara da kira ga jama’a da su ba da hadin kai ga jami’an tsaro da ke aikin tabbatar da doka da oda a jihar.